Hukumar NDLEA a Nijeriya ta kama miyagun ƙwayoyin da aka ɓoye a cikin madubin mota da jan-baki da takalma a wani gagarumin samame da aka gudanar a Legas da Abuja, da wasu jihohin ƙasar.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa jami’an hukumar a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos sun cafke wasu kaya da aka yi niyyar kaiwa Libreville, Gabon, inda aka ga ƙwayoyin Tramadol 57,420 (225mg) da kuma hodar iblis ƙulli 57 da nauyinsu ya kai kilo 1.60 da aka ɓoye a cikin madubin 71.
Hukumar ta ce an kama kayan ne a ranar 19 ga watan inda wanda hakan ya kai ga kama mai jigilarsu Ihekweme Osinachi Benedict.
Hukumar ta zurfafa bincike inda lamarin ya kai ga kama wanda Uzochukwu Godspower Chukwurah, inda aka samu ƙarin hodar iblis guda 11 da nauyinsu ya kai kilo 1.
A wani samame daban, an kama wata ‘yar kasuwa, Nwafor Roseann Nneka, a Dandalin Kasuwar Duniya na Ojo da ke Legas, bayan an gano bi diddiƙin hodar ibilis wadda aka ɓoye a cikin jan-baki da za a tura zuwa Malabo da ke Equatorial Guinea. Mijin ta kuma abokin aikinta, Remigus Nwafor, ya tsere.
A Abuja, jami’an NDLEA sun kama masu aikin kai kaya uku da ke rarraba tabar wiwi nau’in “Canadian Loud” a unguwannin Gwarimpa, Jahi da Galadimawa. Sauran mutane biyu kuma an kama su da tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilo 91.1 a kan hanyar Abaji-Gwagwalada.