Mutum biyar sun mutu a hare-haren da aka kai Birnin Ƙudus

Harin ya faru da safe a Ramot Junction kan titin Yigal, inda aka raunata kimanin mutum 15, kamar yadda wata sanarwa ta baya daga MDA ta bayyana.

Newstimehub

Newstimehub

9 Sep, 2025

e6260888d2ef89fea5d7fa42162b5526f4b3f7a0ace0ec6c592764c4c522e94b

Wasu ‘yan bindiga sun buɗe wuta a tashar mota a Gabashin Birnin Ƙudus da Isra’ila ta mamaye a ranar Litinin, inda suka kashe mutum biyar tare da raunata wasu da dama.

Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta bayyana cewa an kashe ‘yan bindigar biyu a wurin da lamarin ya faru.

Hukumomi sun ce mutum bakwai suna cikin mawuyacin hali.

Cikin waɗanda suka mutu akwai wani mutum mai kimanin shekara 50 da kuma wasu maza uku masu shekaru kusan 30, kamar yadda wata sanarwa daga hukumar agaji ta MDA ta bayyana, tana mai cewa tana ba da kulawar lafiya ga wasu daga cikin wadanda suka ji rauni.

Harin ya faru da safe a Ramot Junction kan titin Yigal, inda aka raunata kimanin mutum 15, kamar yadda wata sanarwa ta baya daga MDA ta bayyana.

Firaminista Benjamin Netanyahu yana gudanar da taro don tantance halin da ake ciki bayan harin, kamar yadda ofishinsa ya bayyana.

“Muna tabbatar da cewa wannan aiki martani ne na halas ga laifukan Isra’ila na mamaye ƙasa da kisan kiyashi da take yi wa mutanenmu,” in ji kungiyar ‘yan gwagwarmaya ta Falasdinawa, Hamas a wata sanarwa.