Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta shiga dandalin sada zumunta na ƙasar, NEXT Sosyal

Matar Shugaban Ƙasar Recep Tayyip Erdoğan Emine Erdoğan ta wallafa saƙon farko a shafinta na NSosyal.

Newstimehub

Newstimehub

19 Aug, 2025

2f487594f524f3dd6f7322bfa60b2a9521e495bbdc40b0fb9283b9d62a5c6188

Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta bayyana a dandalin NSosyal ko NEXT Sosyal, sabon dandalin sada zumunta na ƙasar Turkiyya da aka kaddamar, tare da mika sakon jin daɗi da godiya.

Barkanmu da war haka daga NSosyal. Na yi farin cikin kasancewa cikin wannan dandali namu na gida, na ƙasarmu, da masu zaman kansu, kuma ina mika godiyata ga duk wanda ya kawo wannan alfahari ga al’ummarmu,” ta faɗa a saƙonta na farko da ta wallafa a raar Talata.

A cikin wannan amintacciyar duniyar dijital tamu, za mu yi tunani da samarwa tare, da kuma tsara makomar gaba tare da dabi’unmu. Muna shirye don sabuwar tafiya tare da NSosyal.”

Hawanta dandalin na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bude nasa shafin a dandalin NSosyal.