Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko.

Newstimehub

Newstimehub

21 Aug, 2025

2025 07 24t152548z 1 lynxmpel6n132 rtroptp 3 cocoa ivorycoast

Hukumar da ke kula da harkar noman koko ta ƙasar Ghana (COCOBOD) ta ce manoman koko a ƙasar sun fi takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire samun farashi mai kyau, kuma duk labarin da ya saɓa wa hakan ba gaskiya ba ne.

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba a babban birnin ƙasar Accra ta yi ƙarin haske game da wasu rahotanni da ra’ayoyin jama’ar ƙasar da ke nuna cewa farashin koko daga bakin gona a Ghana bai kai farashin koko ba a  Côte d’Ivoire.

Sanarwar ta ce alƙaluman kasuwa na yanzu da kuma sharhi na masu zaman kansu sun nuna cewa manoman koko na ƙasar Ghana suna samun kuɗi fiye da takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire.

Sanarwar ta ce, rahoton watan Agustan shekarar 2025 na cibiyar da ke sa ido kan saye da sayar da kayayyaki ya nuna cewa farashin da ake sayar da kokon Ghana ya tsaya a kan ¢3,228.75 kan ko wane buhu mau nauyin kilogiram 64 na koko (kwatankwacin ¢51,660 ga ko wane tan ko kuma $5,040.00/ ga ko wane tan).