Gwamnatin Jamus ta yi suka mai tsanani kan shirin Isra’ila na mamaye Gaza, tare da sanar da dakatar da wani ɓangare na fitar da kayayyakin soji zuwa Isra’ila har sai abin da hali ya yi.
“A cikin irin wannan yanayi, gwamnatin Jamus ba za ta amince da fitar da kayan soji da za a iya amfani da su a Gaza ba,” in ji Firaminista Friedrich Merz a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Shugaban mai ra’ayin mazan jiya ya bayyana cewa Jamus ta kasance tana kare hakkin Isra’ila na kare kanta, tana goyon bayan matakan sakin wadanda aka yi garkuwa da su, da kuma kokarin hana Hamas makamai, tare da goyon bayan Isra’ila a duk lokacin rikicin.
“Shawarar Majalisar Ministocin Isra’ila da aka yanke a daren jiya na ci gaba da daukar matakan soji masu tsanani a Gaza na kara wahalar ganin yadda za a cim ma wadannan manufofi daga hangen gwamnatin Jamus,” in ji Merz, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara amincewa da fitar da kayan soji zuwa Isra’ila da za a iya amfani da su a wannan yaƙin ba.