Jami’an tsaro a Somaliya sun kashe ‘yan ta’addan Al Shabab fiye da 50

Jami’an tsaron sun ce sun halaka ‘yan ta’addan ne a wani samame na musamman da suka kai garin Bariire a yunƙurinsu na ƙwato garin

Newstimehub

Newstimehub

4 Aug, 2025

1754302269430 voejfo b3f3d2264698d0e91de3946a82f71a9a9f18c7d1f65d8b60fa8239fb295dd267

Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (AUSSOM) ta bayyana cewa an kashe fiye da ‘yan ta’adda 50 na Al Shabab a wani aikin soji na haɗin gwiwa da sojojin Somaliya a garin Bariire da ke yankin Lower Shabelle.

A yayin wannan aiki, an samu rahoton cewa da dama daga cikin ‘yan ta’addan Al Shabab sun ji munanan raunuka, kamar yadda wata sanarwa daga kungiyar AUSSOM ta bayyana a ranar Lahadi.

“Sojojin AUSSOM da SNAF sun ƙuduri aniyar ƙwato garin Bariire da sauran yankunan da ke ƙarƙashin ikon Al Shabab domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa ga al’ummar Somaliya,” in ji El Hadji Ibrahima Diene wanda shi ne wakili na musamman na Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (SRCC) a Somaliya, a cikin sanarwar.

Haka kuma, ƙungiyar ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa an samu asarar rayuka masu yawa daga ɓangaren sojojinta a wannan aiki.

Bariire wani muhimmin gari ne na noma da ke da tazarar kilomita 73 (mil 45) kudu maso yamma da babban birnin Mogadishu.

Al Shabab, wadda ta shafe fiye da shekaru 16 tana tayar da hankali a Somaliya, tana kai hare-hare akai-akai kan jami’an tsaro, ma’aikatan gwamnati da fararen hula.