Hukumomin Iran sun sanar da kama mutum 500 bisa zargin leƙen asiri tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan ƙasar. Babban hafsan ‘yansandan ƙasar ya ce an kama mutanen ne saboda zargin ba da bayanai ga abokan gaba da kuma kafafen watsa labarai masu hamayya.
A cewarsa, akalla mutum 250 daga cikin waɗanda aka kama ana zarginsu da bai wa kafar Iran International da ke Landan bayanai, ciki har da wuraren da aka kai hare-hare. Hukumomin Iran na zargin waɗannan mutane da taimakawa wajen yaɗa bayanan sirri da kuma tada zaune-tsaye a cikin ƙasar.
An kuma danganta wasu daga cikin waɗanda ake zargin da ƙungiyoyi masu makamai da kuma ƙoƙarin tayar da tarzoma, inda jami’an tsaro suka bayyana su a matsayin masu haɗa kai da abokan gaba domin kawo cikas ga tsaro da zaman lafiya.
Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran ke ci gaba, wanda ya haddasa asarar rayuka da dama da kuma ƙara tsananta rikici a yankin. Iran ma na mayar da martani da kai hare-hare kan wasu ƙasashe da kayayyakin sojin Amurka, lamarin da ke ƙara tayar da hankulan duniya.
Tushen labari: Newstimehub









