INEC ta buƙaci a hukunta duk wanda ya fara kamfen ɗin 2027 kafin lokaci

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta Nijeriya (INEC) ta bukaci da a yi sauye-sauyen dokoki da daukar matakai masu tsauri kan ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da suke fara gangami da wuri tun kafin lokacin manyan zabukan 2027 ya zo.

Newstimehub

Newstimehub

10 Sep, 2025

al48etz5 400x400 1

Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, a yayin da yake magana a Abuja, a wajen wani taro kan kalubalen yakin neman zabe da wuri, ya koka kan yadda hukumar ba ta da hurumin hukunta masu laifi.

Yakubu ya bayyana damuwarsa da cewa ‘yan siyasa da ‘yan takararsu sun jefa al’ummar kasar cikin “dawwamammiyar kakar zabe,” wanda hakan ya saɓa wa sashe na 94(1) na dokar zabe ta 2022, wanda ya ba da damar yakin neman zabe kwanaki 150 kacal kafin zaben.

Duk da wannan doka, shugaban na INEC ya yi tsokaci da cewa ’yan siyasa na ci gaba da mamaye wuraren jama’a da tallace-tallacen kafafen yada labarai, da gangami, da allunan ttallace-tallacen takarar zabukan 2027 da kuma zabukan fitar da gwani da ke tafe.

Ya ce an kira taron ne domin a bukaci ‘yan majalisar dokoki, kungiyoyin farar hula, masu kula da harkokin shari’a da kuma masana harkokin shari’a su lalubo bakin zaren.