Ghana ta karɓi ‘yan Nijeriya da aka kora daga Amurka – Mahama

Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ya kasance ɗan ƙasar Gambiya.

Newstimehub

Newstimehub

11 Sep, 2025

1741769933186 vbe01p 2024 12 14t124637z 684040865 rc2f 9 rtrmadp 3 ghana politics mahama

Ghana ta tabbatar da isowar kashin farko na ‘yan Yammacin Afirka da aka kora daga Amurka a ƙarƙashin yarjejeniyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba John Mahama, wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar Jubilee House ranar Laraba, ya ce mutum 14 ne jirgin sama ya kai ƙasar a wani ɓangare na yarjejeniyar.

Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ɗan ƙasar Gambiya ne.

“Hukumomin Amurka sun yi mana tayin karɓar ‘yan wasu ƙasashe da ake so a fitar daga ƙasarsu sannan muka amince cewa za mu karɓi ‘yan Yammacin Afirka saboda dukkan ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka ba sa buƙatar izinin shiga ƙasarmu. Saboda haka idan sun zaɓi tafiya daga Amurka zuwa Accra ba sa buƙatar izinin shiga ƙasar. Saboda haka idan za ka dawo da ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka, ya yi daidai,” in ji Shugaban ƙasar.

Ya ƙara da cewa Ghana ta taimaka wajen mayar da ‘yan Nijeriya ƙasarsu ta hanyar ba da motar bas da za ta kai su gida.