Rahotanni na cewa fitaccen tsohon ɗanwasan ƙwallon ƙafa na Brazil kuma tsohon tauraron Real Madrid da Fenerbahçe Roberto Carlos ya musulunta a Brazil kimanin makonni huɗu da suka gabata, a cewar wani ɗan majalisar dokokin Turkiyya yana ambato wani fitaccen shugaban al’ummar Musulmi a Brazil.
Ali Şahin, ɗanmajalisa daga jam’iyyar AK mai mulkin Turkiyya ya bayyana haka bayan ganawa da wakilan al’ummar Musulmin Brazil a Sao Paulo.
Şahin ya ce ya ji labarin musuluntar Carlos daga bakin Sheikh Jihad Hammadeh, wani fitaccen jagora a cikin al’ummar Musulmin Brazil, wanda mmataimakin shugaba ne sannan mai ba da shawara kan addini a Kwamitin Fatawar Addini Musulunci ta Ƙasa (ANAJI).
A cewar Şahin, Hammadeh ya faɗa masa cewa Carlos ya daɗe yana mu’amala da shi kuma ya ziyarce shi kimanin makonni huɗu da suka gabata, lokacin da tsohon ɗanwasan ya furta kalmar shahada, sannan ya rungumi Musulunci.
Şahin ya sanar da hakan a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta bayan ganawa da Hammadeh da sauran wakilan al’ummar Musulmin Brazil a Cibiyar Ƙungiyar Matasa Masu Aikin Gudunmawa ta Musulunci ta Brazil da ke Sao Paulo.
Ya taya Carlos murna bisa yadda aka ruwaito ya rungumi Musulunci, kuma ya yi masa fatan zaman lafiya, da lafiya da wadata.
Wakilan kungiyoyin Musulmi da dama a Brazil sun halarci taron, ciki har da Shugaban Kungiyar Matasan Masu Aikin Gudunmawa ta Musulunci, Charif Neto, da Shugaban Gidauniyar Masallacin Pari, Omar Aref, da wakilan ANAJI da sauran kungiyoyin agaji da ilimi na Musulunci.
A baya bayan nan ne Roberto Carlos ya auri Suhayla At Tohiri, wata fitacciyar wakiliyar ƙwallon kafa ‘yar asalin ƙasar Maroko da ke zaune a Sifaniya.
Ana daukar Carlos, mai shekaru 53, a matsayin ɗaya daga cikin manyan ‘yanbaya a ɓangaren hagu a tarihin kwallon kafa. Dan Brazil ɗin ya shafe mafi yawan lokacinsa a Real Madrid kafin ya koma Fenerbahçe a Turkiyya a shekarar 2007.
Har kawo yanzu dai Carlos da kansa bai tabbatar da cewa ya musulunta a bainar jama’a ba.















