Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, sun tattauna kan sakamakon taron da aka gudanar a birnin Washington tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da sauran Shugabannin Turai.
A wata tattaunawar wayar tarho da suka yi a ranar Talata, sun kuma tattauna kan sakamakon taron da aka yi tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Alaska a ranar 15 ga watan Agusta, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka bayyana.
Sun yi magana kan matakan da za a iya dauka nan gaba don kawo karshen yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, inda Fidan ya bayyana cewa a shirye Turkiyya take ta bayar da duk wani irin tallafi don cim ma zaman lafiya mai adalci da ɗorewa.
A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott jami’an biyu sun amince kan bukatar dakatar da kashe-kashe tsakanin kasashen biyu da ke fada.
Ci gaba da goyon bayan zaman lafiya a Ukraine
Mataimakin Shugaban Turkiyya, Cevdet Yilmaz ya bayyana a ranar Talata cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen diflomasiyya da nufin cim ma “zaman lafiya mai adalci da ɗorewa” a Ukraine.
“Za mu ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga kokarin diflomasiyya don zaman lafiya mai adalci da dorewa,” in ji Yilmaz a dandalin sada zumunta na Turkiyya, NSosyal.