Somalia ta yi watsi da amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland a matsayin barazana ga yankin

Somalia ta ce matakin na Israila ya raina ‘yancin kanta, yayin da Masar, Saudiyya, Ƙungiyar Haɗin Kan Larabawa da Tarayyar Afirka suka bayyana goyon baya ga tabbatar da cikakken ‘yancin kan ƙasar.
27 Dec, 2025
Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma

Falasɗinawa mabiya addinin Kirista sun gudanar da bikin Kirsimeti a karon farko tun 7 ga Oktoban 2023, lamarin da ya sa aka dakatar da bikin saboda hare-haren Isra’ila a Gaza da Gaɓar Yamma.
25 Dec, 2025
Babban hafsan sojin Libya da jami’ai sun mutu a hatsarin jirgin sama a kusa da Ankara: Dbeibah

Hukumomin Turkiyya sun ce an daina jin ɗuriyar jirgin saman na Falcon 50 wanda yake na haya ne da ke kan hanyar zuwa Tripoli bayan ya bayar da rahoton wata matsala a kusa da tsakiyar Turkiyya.
24 Dec, 2025
Trump ya saka ƙasashen Afirka biyar cikin jerin da ya haramta wa shiga Amurka

Matakin na ranar Talata ya haramta wa ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Sudan ta Kudu da Syria da kuma masu riƙe da takardar tafiya ta hukumar Falasɗinawa
17 Dec, 2025

An kashe sojojin Bangladesh da ke aikin wanzar da zaman lafiya a sansanin MDD na Sudan: Bangladesh

China ta zartar da hukuncin kisa kan tsohon ma’aikacin banki kan karɓar cin hancin dala miliyan 156

Venezuela ta rantsar sabbin sojoji 5,600 yayin da rikici tsakaninta da Amurka ke ƙara tsami

Hotuna: Dubban mutane sun yi maci a Turai da Amurka don nuna wa Falasdinawa goyon baya

Mutane sama da 100 sun mutu, da yawa sun ɓata a mummunar ambaliyar da ta addabi Sumatra, Indonesia
27 Nov, 2025
An kama wani ɗan Afghanistan bayan harbin sojojin rundunar tsaron ƙasa kusa da Fadar White House
Amurka ta dakatar dukkan aikin bai wa ‘yan Afghanistan iznin shiga ƙasar har sai an gama shirye-shiryen nazari kan tsarin tattancewa da na tsaro.

27 Nov, 2025
Fafaroma Leo XIV ya isa Turkiyya a ziyararsa ta farko ƙasar waje, don jaddada zaman lafiyar duniya
An- shirya cewa Fafaroma zai gana da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da ziyartar birane masu girma da kuma tattaunawa kan ayyukan addini.

27 Nov, 2025
Miji ko saurayi ko ‘yan’uwa na kashe mace ɗaya cikin kowane minti 10 a duniya: Rahoton MƊD
Kimanin mata da ‘yan mata 50,000 a faɗin duniya na kusa da su suka kashe a shekarar 2024, lamarin da ke nufin ana kashe mata da ‘yan mata 137 ko wace rana, in ji wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya.

26 Nov, 2025
Rasha ta ce a shirye ta ke ta taimaka wa Nijeriya a yaƙi da ta’addanci
Moscow ta ce Nijeriya tana da ‘cikakkiyar kwarewa’ wajen magance barazanar tsattsauran ra’ayi, ta yi alƙawarin taimakawa.

25 Nov, 2025
Sojojin Isra’ila suna ci gaba da rusa gidaje da harba makaman atilare Gaza, duk da tsagaita wuta
Rahotannin na zuwa ne a daidai lokacin da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza da MDD suka yi gargaɗin cewa ana ci gaba da kisa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta 10 ga Oktoba, inda aka kashe Falasɗinawa fiye da 340 aka kuma jikkata kusan 900.

19 Nov, 2025
Ukraine ta harba wa Rasha makami mai linzamin ATACMS da aka kera a Amurka yayin da yaki ya tsananta
Garkuwar tsaro ta Rasha ta tare makamin mai linzami na Ukraine mai tsananin gudu da aka harba shi zuwa birnin Voronezh, inda aka dakile ta’adinsa, yayin da ya lalata wasu gine-gine.

19 Nov, 2025
Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya ya samu tarba mai kyau daga Trump a Fadar White House
Shugabannin biyu za su bayyana yarjejeniyar biliyoyin daloli, ciki har da ta sayar wa jiragen yakin F-35 na Riyadh, sannan su yi zama da mataimakansu don tattauna hanyoyin warware matsalolin Gabas ta Tsakiya kafin wani taron manema labarai.

17 Nov, 2025
Trump ya sayi takardun lamuni na aƙalla dala miliyan 82 tun daga Agustan 2025 – Bayanai
Bayanai sun nuna cewa Trump ya sayi takardun lamuni a kamfanonin da suke amfana da munfofi da tsare-tsaren gwamnatinsa waɗanda suka haɗa da kamfanin Meta, Qualcomm da JP Morgan da wasu jerin kamfanoni.

17 Nov, 2025
Koriya ta Kudu ta nemi yin tattaunawar soji da Koriya ta Arewa don kaucewa rikicin kan iyaka
Seoul ta yi kira da ayi tattaunawar soji ta Korea da nufin rage zaman ɗar-ɗar da kuma fayyace layin kwance ɗamara, bayan sojojin Korea ta Arewa sun ringa tsallake iyaka ba sau ɗaya ba sau biyu ba.

15 Nov, 2025
Trump ya bayar da umarnin haramta wa masu ƙiba shiga Amurka
Wannan shi ne sabon matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka don ƙin yarda da baƙin-haure a matsayin wani ɓangare na matakansa na taƙaita shige da fice.


