Cristiano Ronaldo ya zama ɗanwasa na farko da ya zura ƙwallo a raga a Gasar Cin Kofin Duniya shida

Kyaftin ɗin mai shekara 41 ya samu ya sake zura ƙwallo a raga minti shida da fara wasa a karawar Portugal da Uzbekistan a Houston, inda ya zama ɗan wasa na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ya zura ƙwallaye a raga a Gasar Cin Kofin Duniya shida.

Newstimehub

Newstimehub

24 Jun, 2026

uzbekistan portugal wcup soccer 74734

Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallaye a raga a Gasar Cn Kofin Duniya shida, inda ya rufe bakin masu suka bayan “baƙin mako” inda kyaftin ɗin na Portugal ya zura ƙwallo biyu a raga yayin da tawagarsa ta lallasa Uzbekistan da ci 5-0.

Babbar nasarar a Houston a ranar Talata ta kai Portugal dab da matakin sili-ɗaya-ƙwale kuma wani babban martani ne ga masu shakka kan ɗanwasan mai shekara 41.

Ƙwallon da Ronaldo ya zura bayan minti shida da fara wasan ta kafa tarihi — wanda ya zarce na Lionel Messi ma — ta hanyar zura ƙwallaye a raga a Gasar Cin Kofin Duniya shida daga shekarar 2006.

Tsohon ɗanwasan Manchester United da Real Madrid da Juventus ya fito da salon murnar cin ƙwallonsa na “Siu” kuma ya ƙwalla ihu a gaban magoya baya 68,777 .

Bayan Nuno Mendes ya zura ƙwallo ta biyu a 2-0, Ronaldo ya samu ƙwallonsa ta biyu ta hanyar zura ƙwallo a hankali, minti shida kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Wannan shi ya mayar da ƙwallayen da ya zura a gasar cin kofin duniya ya kai 10, fiye da adadin ƙwallayen da duk wani ɗan wasan Portugal ya taɓa zurawa a tarihin gasar ciki har da na gwarzo Eusebio.

An ga Ronaldo yana cewa , “na dawo, na dawo”, kuma ya shaida wa kafofin watsa labarai cewa : “A ko da yaushe abu mai kyau ne mutum ya kafa tarihi, amma burina shi ne na taimaka wa tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa cim ma buƙatunta.”

Ya ƙara da cewa: “Baƙin mako ne, mai wahala. Ya yi kamar na riga na yi ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa .

“Amma na ci gaba, kamar kullum, domin na fi imani cikin aiki tuƙuru fiye da komai.

“Yana da wahala, dole na amince da hakan, amma mun dawo.”

Ronaldo ya shiga karawar a rukuni ɗaya da ƙasar da ke shiga gasar a karon farko, Uzbekistan, yana da ƙwallaye 143 da ya zura a raga, yawancinsu ya zura su ne ga tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasarsa.

Amma ɗanwasan da a da ana masa kallon abokin gogayyar Messi wajen kasancewa ɗanwasan da ya fi ƙwarewa a idon mutane, ƙarfinsa ya fara raguwa a mataki mafi ƙololuwa.

Ya kasa gamsar da mutane da yawa a wasan da ƙasarsa ta tashi 1-1 da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ƙasar ta fara neman cin gasar cin kofin duniya ta bana .

Amma a lokacin da ya samu damarmaki biyu na zura ƙwlalaye a raga, ya gaza zura ƙwallayen, lamarin ya fara haddasa kiraye-kiraye ga koci Roberto Martinez ya ajiye shi a benci.

Matsalolinsa wajen zura ƙwallaye a raga sun bayyana ƙarara idan aka kwatanat da yanayin irin su Messi da Kylian Mbappé da Erling Haaland da kuma Harry Kane, waɗanda taurarinsu suka haskaka daga farkon Gasar Cin Kofin Duniyar.

Amma Martinez ya dage da amfani da kyaftin ɗinsa , wanda aka yi maraba da shi cikin ihu a lokacin da ya fito atisayen fara wasa a filin wasan Houston da kuma duk lokacin da aka nuna shi a manyan alluna.

Ranar Ronaldo

Ronaldo ya kusa jefa ƙwallo bayan minti uku da fara wasa, inda ƙiris ya kusa ya taɓa ƙwallo kusa da raga bayan Mendes ya yiyo kurosin. Ronaldo ya yi dukan iska a cikin filin wasa a cikin taƙaici.

Bai jira da yawa ba kafin ya sami ƙallonsa, inda ya zura ƙwallo a raga ta wani kurosin da Joao Cancelo ya yiyo kuma ya zura ƙwallon ya wuce gola Abduvohid Nematov.

Tawagar Uzbekitan ɗin da aka fi ƙarfinsa, wanda kocin tawagar Italiya da ta ci gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006 Fabio Cannavaro, ya jagoranta su ne abokan gaba da suka fi dacewa wajen bai wa Ronaldo damar sake gano dabarun zura ƙwallayensa a raga.

Wasa ya zama 2-0 minti 17 da fara wasa a lokacin da Mendes ya zuro wani bugun tazara.

‘Yan Uzbekistan sun yi tsammanin cewa sun goge ƙwallo ɗaya, bayan Azizjon Ganiev ya buga ƙwallo da ƙarfin gaske, amma an soke ƙwallon bayan VAR ta tabbatar da cewa an yi wa Cancelo ƙeta.

Ranar Ronaldo ce, kuma ya zura wa Portugal ƙwallonta na uku inda ya zura ƙwallo a raga ta hanyar yanke golan.

Da zai ci ƙwallo na uku bayan wani bugun tazara mai sarƙaƙaiya, amma Nematov ya hana shi , inda ya ci karo da daɗaɗɗen ɗan wasan gaban.

Daga kwanan da aka buga sakamakon wannan wasan ya zama 4-0, inda Ronaldo ya sake kasancewa cikin ƙoƙarin kafin ƙwallon ya shiga raga bayan ya bar wajen Nematov, wato ƙasar Uzbekistan ta ci kanta .

Wanda ya shiga wasa bayan an fara wasa Rafael Leao ya zura ƙwallo na biyar a raga minti 87 da fara wasa .

Wasan ranar Talata shi ne wasa na 230 da Ronaldo ya buga wa ƙasarsa, wanda shi ne adadin wasanni mafi yawa a tarihi.

A wasanni 10 na baya da ya buga a muhimman gasa (gasar cin kofin duniya da ta Turai) kafin wasan Uzbekistan, bai ci ƙwallo ko ɗaya ba kuma ya taimaka wajen cin ƙwallo ɗaya .

Amma ya samu kaka mai nasara a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Nassr a Saudiyya, inda ya zura ƙwallaye 28 a raga a wasannin gasar lig 30 .

Wasan Portugal na ƙarshe a matakin rukuni za ta buga shi ne ranar Asabar da Colombia, wadda ta doke ‘yan Uzbekistan da ci 3-1.
Colombia za ta kara da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo daga baya ranar Talata a wasan rukuni na K inda suka san cewa nasara za ta kai su cikin ƙasashe 32 na ƙarshe.