Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa

Burkina Faso tace matakin ya fara aiki daga ranar 26 ga watan Yuni, kuma ya biyo bayan nazari kan duk wata dangantaka da birnin Paris.

Newstimehub

Newstimehub

27 Jun, 2026

feee88b62f7f09b726e3fdf4e3b51d110d43786b08a4b900368c759fdc6c1d3f

Burkina Faso ta faɗa a ranar Juma’a cewa ta yanke hulɗar diflomasiyya da tsohuwar ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa, bayan shekaru ana samun rashin jituwa, tana mai zargin Paris da ci gaba da yin ayyuka saɓanin muradun ƙasar.

“Gwamnatin Burkina Faso ta sanar wa al’ummar ƙasa da ta duniya cewa ta yanke shawarar katse hulɗar diflomasiyya da Faransa, daga yau, 26 ga Yuni, 2026,” kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar ta Yammacin Afirka.

“Ba a samar da muhimman sharuɗan da za su inganta alaƙa bisa mutunta juna, da amincewa juna, da girmama ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gida, da kuma ƙarfafa matsayin ɗan ƙasa ba,” in ji Ministan Sadarwa Gilbert Ouedraogo.

Ouedraogo ya ce matakin ya fara aiki a ranar 26 ga Yuni kuma ya biyo bayan sake yin nazari kan dangantaka da Paris.

Ya zargi Faransa da tallafa wa “ƙungiyoyin da ke zagon ƙasa” da “‘yanta’adda”.

Ba sa mu ma’aikatar harkokin wajen Faransa ba nan-take don ta yi tsokaci kan matakin, ko da yake ta riga ta musanta zarge-zargen da ake mata na tallafa wa ta’addanci.