Gwamnatin Australiya ta soke bizar wani ɗan siyasar Isra’ila mai ra’ayin riƙau a ranar Litinin gabanin wani rangadi da zai je ƙasar, matakin da masu shirya taron suka kira “ƙiyayya mai tsanani ga Yahudawa.”
Simcha Rothman, wanda jam’iyyarsa tana cikin haɗin gwiwar gwamnatin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, an tsara zai yi jawabi a tarukan da Ƙungiyar Yahudawan Australiya ta shirya.
Amma Ministan Harkokin Cikin Gida, Tony Burke, ya ce Australiya ba za ta karɓi mutane da ke zuwa ƙasar don “haddasa rarrabuwar kai ba”.
“Idan kana zuwa Australiya don yaɗa saƙon ƙiyayya da rarrabuwar kai, ba ma son ka nan,” in ji shi. “Australiya za ta kasance ƙasa inda kowa zai iya zama lafiya, kuma kasance cikin aminci.”