A ranar Asabar ɗin nan ne ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu da ke sassa daban-daban a faɗin Nijeriya, waɗanda ake gani za su ƙara fito da ƙarfi ko akasin haka na Jam’iyyar APC mai mulki da kuma Jam’iyyun adawa na ƙasar.
Ana gudanar da zaɓukan ne a mazaɓu goma sha shida a jihohi 13 – Adamawa, Anambra, Edo, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Ogun, Oyo,Taraba da Zamfara.
Zaɓukan da za a cike gurbinsu sun haɗa da na ‘yan majalisar dattawa da majalisar wakilai da majalisun dokoki na jihohi.