Masana ilmin kayan tarihi sun tono wani sassaƙen dutse mai shekaru 11,000 wanda ke nuna wani mutum zaune a bayan damisa a Karahantepe, ɗaya daga cikin rukunin wuraren tarihi a kudu maso gabashin Turkiyya wanda ke sake fasalta fahimtar matsugunan mutane na farko.
An gano sassaƙen mai tsawon santimita 70 a lokacin haƙa rami a wannan shekarar a Karahantepe, kusa da birnin Sanliurfa, in ji Ministan Al’adu da Yawon Bude Ido na Turkiyya Mehmet Nuri Ersoy a ranar Talata.
A cikin wani rubutu da ya yi ta shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal, Ersoy ya bayyana aikin a matsayin sassaƙen da ba a taɓa gani a wurin ba. An same shi a kan benci yana ajje a gefen bangon wani gini mai tsawon mita 3, wanda aka lulluɓe dandamalinsa da duwatsu masu faɗi, in ji shi.
Gano wannan sassaƙe wani ɓangare ne na aikin tono-tonen da Turkiyya ke ci gaba da yi a ƙarƙashin aikinta na “Kayan Gado zuwa Makoma”, wanda ke da nufin faɗaɗa binciken kayan tarihi da adana su a wuraren da suke a faɗin kasar.
Karahantepe wani yanki ne daban na tarihi, da ke a nisan kimanin kilomita 30 daga Gobeklitepe, kuma ɗaya daga cikin wurare sama da goma sha biyu a yankin da aka fi sani da Tas Tepeler, ko “Tuddan Duwatsu,” a aikin kayan tarihi.
Wuraren sun samo asali ne daga zamanin Neolithic, sama da shekaru 10,000 da suka gabata, lokacin da al’ummomin yankin ke canzawa daga salon rayuwa na mafarauta masu motsi zuwa ga rayuwa mafi kwanciyar hankali.
Gine-ginen duwatsu masu ban mamaki, sassaka da sauran kayan da suka rage sun zama shaidar ayyukan zamantakewa da na al’ada masu rikitarwa tun kafin samuwar birane da rubuce-rubuce.
Gobeklitepe, wanda aka gano a shekarun 1960 kuma aka tono shi sosai tun shekarun 1990, shi ne mafi shahara a cikin wuraren. Manyan ginshiƙan dutse masu siffar T da sassaken dabbobi sun ƙalubalanci zato na baya game da ci gaban matsugunai na dindindin da al’ummu masu tsarin rayuwa.
Karahantepe ya zama wani muhimmin wuri a yankin tun lokacin da aka fara tono ƙasa a wajen a shekarar 2019. Masana ilmin kayan tarihi sun gano gine-gine masu tarihi, abubuwa da ke nuna wanzuwar mutane da dabbobi da sauran al’amuran da suka faru kamar dai yadda yake a Gobeklitepe.
Ersoy ya ce gano sassaken “ta bude kofa ga sabbin tambayoyi game da farkon zamanin tarihin ɗan adam” kuma zai yi tasiri mai yawa ga masana kimiyya.















