Shugaba Tiani na Nijar ya ce har yanzu Faransa ba ta daina yi musu bi-ta-da-ƙulli ba

Shugaban Tiani ya zargi Faransa da hannu a kusan duka rikice-rikicen da suka faru a ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Pakistan da Afghanistan da Iraƙi da Syria da Libiya.
1 Jun, 2025
Mutum fiye da 1,300 sun kamu da cutar kwalara a cikin kwana guda a Sudan

Ko a ranar Laraba sai da ma’aikatar lafiya ta Jihar Khartoum ta sanar da samun mutum 942 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutum 25 a ranar Talata, yayin da a ranar Litinin aka samu mutum 1,177 da suka kamu da cutar da mutuwar mutum 25.
30 May, 2025
Sidi Ould Tah ya zama sabon Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka AfDB

Masanin tattalin arzikin mai shekaru 60 da haihuwa shi ne na ƙarshe da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara kuma ya gudanar da yakin neman zaɓe inda ya bayyana shekaru 10 da ya yi a matsayin Shugaban Bankin Larabawa na Bunkasa Tattalin Arzikin Afirk
29 May, 2025
An yanke wa wata mata ‘yar Afirka ta Kudu hukuncin daurin rai da rai saboda sayar da ‘yarta

An yanke wa Racquel Smith da wasu mutane biyu da aka gurfanar da su tare hukuncin daurin rai da rai saboda safarar bil’adama, da kuma hukuncin shekara 10 saboda satar mutane
29 May, 2025

ECOWAS ‘tana da ƙwarin gwiwar’ cewa Burkina Faso, Mali da Nijar za su koma cikin kungiyar

Muhimman abubuwan da suka kamata ku sani game da tarihin ECOWAS

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu sun kori jakadan Isra’ila daga harabar jami’ar Senegal

Cutar kwalara ta yi ƙamari a Sudan yayin da yaƙi yake hana kula da marasa lafiya

Ɗaruruwan mutane sun kamu da cutar kwalara a Sudan
24 May, 2025
Nijar ta kori duka ‘yan ƙasashen waje da suka shafe shekara huɗu suna aiki a kamfanin mai na CNPC
Gwamnatin Nijar ta bayar da wa’adin 31 ga Mayun 2025 ga duka ma’aikatan su fice daga ƙasar, kamar yadda wata wasiƙa da Ministan Man Fetur na Nijar Dakta Sahabi Dumarou ya aika wa kamfanin ta nuna.

23 May, 2025
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta cire wa tsohon shugabanta Joseph Kabila rigar kariya
Ana zargin Kabila a DRC da aikata laifukan cin zarafin ɗan’adam, musamman goyon bayan tawaye a gabashin ƙasar, ciki har da rawar da ake zargin ya taka a kisan gilla na fararen hula da ma’aikata

23 May, 2025
Masu hakar ma’adanai kusan 300 sun makale a karkashin kasa a Afirka ta Kudu
Kakakin kamfanin haƙar ma’adanan na Sibanye ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci.

23 May, 2025
Amurka za ta saka wa Sudan takunkumi kan zargin amfani da makamai masu guba
Ana sa ran takunkumin zai fara aiki a ranar 6 ga watan Yuni, bayan an wallafa shi a cikin kundin bayanai na Amurka.

22 May, 2025
Abu biyar da suka faru a tattaunawar Trump da Shugaban Afirka ta Kudu, Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce ya ji daɗin taron bayan da kwanton ɓaunar Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, wanda ya yi kamar yadda Shugaban Amurka ya yi wa Shugaban Yasar Ukrain Volodymyr Zelenskyy da suka gabata

22 May, 2025
ECOWAS na duba yiwuwar kafa runduna yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke kara yawaita
ECOWAS ta ce shirye-shiryen kafa “rundunar yaƙi da ta’addanci a yankin” da aka daɗe ana jira “sun kankama” yayin da Yammacin Afirka ke yaƙi da farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda.

20 May, 2025
An yi wa shafin rundunar ‘yan sandan Tanzania kutse an sanar da mutuwar Shugabar Ƙasa Samia
‘Yan sandan sun ce “labarin ƙaryar”, wanda tuni aka cire shi daga shafin nasu, wasu masu kutse ne suka wallafa shi tun farko.

20 May, 2025
An samu akalla gawawwaki 58 da ba a tantance su ba a wani asibiti a Libya
Minsitan cikin gida na Libya ya ce an gano gawawwakin ne a wajen adana gawawwaki a wata mutuware a Asibitin Abu salim a birnin Tarabulus

19 May, 2025
Shugaban soji na Sudan, Burhan ya naɗa sabon firaministan ƙasar
Shugaban Majalisar Tsaron Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya naɗa Kamil El-Tayib Idris, wani tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya, a matsayin Firaministan Sudan.

19 May, 2025
Kotun MDD za ta yanke hukunci kan rikicin Gabon da Equatorial Guinea kan yankuna masu arzikin mai
Rikicin dai ya samo asali ne tun a shekarar 1900, lokacin da ƙasashen Faransa da Sifaniya da suka yi mulkin mallaka suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Pariskan da nufin samar da iyakokin ƙasashen biyu.
