Ambaliyar ruwa da aka yi a wurare daban-daban a Jamhuriyar ta kashe mutum 81 da jikkata mutum 131 tare da shafar mutum 97,334 ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoban 2026, kamar yadda Ministan Kula da Yawan Jama’a da Matakan Zamantakewa, Sani Douda, ya bayyana.
Kamfanin Dillancin labaran Nijar (ANP) ya ba da rahoton cewa an bayyana wannan ne a wajen buɗe taron nazari kan yadda aka tafiyar da ambaliya ta shekarar 2026 a Maradi ranar Talata.
Taron wanda aka yi a ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Maradi, Sufeto Janar na ‘Yansanda Issoufou Mamane, a ɗakin taron otel ɗin Guest House, an yi shi ne don nazari kan matakan da aka ɗauka a cikin shekarar don gano gazawa da kuma gabatar da shawarwari don inganta hana aukuwar ambaliya da kuma magance ta a shekarar 2027, in ji ANP.
A nasa jawabin, gwamnan Jihar Maradi ya yaba wa jajircewar hukumomi a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani da kuma Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine, wajen inganta yanayin rayuwar jama’a da ƙarfafa juriyarsu yayin da suka fuskanci masifun yanayi.
Ya jaddada muhimmancin yin taron bitar kuma ya bayyana gamsuwarsa da zaɓar Jihar Maraɗi a matsayin mai karɓar baƙuncin tarukan.
Sani Douda ya bayyana cewa adadin waɗanda ambaliya ta kashe zuwa ranar 31 ga watan Oktoba sun kai mutum 81, kuma ta shafi iyalai 13,976 tare da shafar ɗaiɗaikun mutane 97,334 da kuma jikkata mutum 131.
Ya ƙara da cewa gidaje 12,985 ne suka rufta sakamakon ambaliyar yayin da dabbobi 1,366 suka salwanta.
Ya jaddada cewa ƙoƙarin da aka yi a cikin shekarar sun mayar da hankali ne kan ƙarfafa sa ido da kuma tsare-tsaren ba da gargaɗi da wuri da shirin aiki da wayar da kan jama’a.
Sani Douda ya bayyana cewa nazarin zai ba da damar tunanin kan matakan da aka ɗauka da gano kurakurai da da kuma koyon darrusa masu muhimmanci wajen inganta hana aukuwar ambaliya da tafiyar da ambaliya a shekarar 2027.
Daga bisani, ya yi kira ga mahalarta taron su bayar da shawarwari masu ɗorewa don ƙarfafa hana aukuwar masifu da tsare-tsaren tafiyar da lammura.
A nasa ɓangaren, wakilin WFP Ofishin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), shugaban ma’aikatan WFP a Nijar, Gaspard Cirhalwirwa, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Nijar tare da jajircewar hukumomi da al’ummomi da masu ruwa da tsaki wajen hana aukuwar masifu da magance su.
Ya bayyana cewa wannan taron bitar aikin wata dama ce ta koyon darrusa daga yadda aka tafiyar da ambaliya ta shekarar 2026 don ƙarfafa yadda za a tunkari shekarar 2027.
Gaspard Cirhalwirwa ya jaddada jajircewar WFP ga tallafa wa gwamnatin Nijar wajen hana aukuwar masifu da magance su, musamman ta hanyar ƙarfafa tsare-tsaren ƙasa da ikon shiri da juriyar al’umma.















