Nijar ta shirya taron zuba jari na ƙasa da ƙasa karo na farko, da neman jarin CFAF triliyan 5.5

Masu shirya taron za su gabatar da ayyukan zuba jari guda 50 a fannoni 13 masu muhimmanci, ciki har da noma, da kiwo, da hakar ma’adinai, da makamashi, da sufuri, da ababen more rayuwa, da fasahar zamani da sauransu.

Newstimehub

Newstimehub

25 Nov, 2026

8de2ac5a 5dd9 425a b842 7bb15a848a27 1795600426912

Jamhuriyar Nijar ta ɓude wani taron zuba na ƙasa da ƙasa, inda za ta nemi jarin CFAF tiriliyan 5,500, wato kwatankwacin dala biliyan 9.6, a wani ƙokari da take yi na bunkasa tattalin arzikinta tare da jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na waje.

An buɗe taron F2IN 2026 da ke gudana a cibiyar taro na kasa da kasa ta Mahatma Gandhi dake birnin Yamai, babban birnin kasar a ranar Talata 24 ga Nuwamba kuma za a kwashe kwanaki uku ana yi.

A cewar Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Raya Ƙasashe (UNDP), wanda ke tallafa wa shirin, ana sa ran taron zai samu halartar kusan mutane 1,000, ciki har da masu zuba jari 300 daga ƙasashe akalla 300, da wakilan gwamnati, da cibiyoyin hada-hadar kudi da shugabannin kamfanoni masu zaman kansa.

Masu shirya taron za su gabatar da ayyukan zuba jari guda 50 a fannoni 13 masu muhimmanci, ciki har da noma, da kiwo, da hakar ma’adinai, da makamashi, da sufuri, da ababen more rayuwa, da fasahar zamani, da yawon bude ido, da kiwon lafiya da kuma bunkasa masana’antu.

Ministan Kasuwanci da Masana’antu na Nijar, Abdoulaye Seydou, ya ce manufar taron ita ce bude wani sabon babi a ƙokarin da gwamnatin Nijar ke yi na bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar kulla kawance da kuma jawo jarin da zai samar da ci gaba mai dorewa.

Ya bukaci masu zuba jari da su yi amfani da damar da ake da ita wajen duba muhimman fannoni, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen gina Nijar mai wadata da kuma karfin tattalin arziki.

Kazalika wakilin UNDP a Nijar, Mamadou N’Daw, ya ce zuba jari mai yawa daga kamfanoni masu zaman kansu na da matukar muhimmanci wajen bunkasa damar da kasar ke da ita, tare da samar da ayyukan yi da kuma karfafa tattalin arzikinta.

A yayin taron, za a tattauna kan manufofin zuba jari da yanayin kasuwanci, tare da gabatar da ayyukan da za a saka kuɗaɗe wajen gudanar da su. Haka kuma, za a gudanar da tarurrukan masu zuba jari da wakilan gwamnati, da kuma na kamfanoni domin lalubo hanyoyin haɗin gwiwa.

Ana kuma sa ran mahalarta taron za su kai ziyara wasu wuraren da aka ware domin ayyukan zuba jari, don tantance damarmakin da ake da su da kuma duba yiwuwar kulla kawance.

Ko da yake adadin kuɗin CFAF triliyan 5,500 da aka ambata, wani kudurin zuba jari ne da Nijar ke fatan jawo wa ta wannan taro, ba kudaden da aka riga aka tara ko aka kashe ba. Nasarar shirin za ta dogara ne da yadda za a mayar da yarjejeniyoyin da aka cim ma zuwa hakikanin hanyoyin zuba jari da kuma kammala ayyukan da aka tsara.