An wallafa jawabin da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gabatar a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a matsayin littafi cikin harsunan Turkanci da Ingilishi da kuma Larabci, inda aka mayar da jawabinsa kan rikice-rikicen duniya da gyare-gyaren tsarin dokokin ƙasa da ƙasa zuwa wani littafi na dindindin.
Littafin, wanda fadar shugaban ƙasar Turkiyya ta fitar a ranar Laraba, ya tattara sakonnin Erdogan game da Gaza da rikice-rikicen yankuna da yaƙin Rasha da Ukraine da kuma abin da ya bayyana a matsayin gazawa a tsarin dokokin duniya a yanzu.
An gabatar da littafin ne ƙarƙashin taken “Yiwuwar Samun Duniya Mai Adalci.”
Jawabin shugaban wanda ya gabatar a birnin New York a ranar Talata, ya fi mayar da hankali kan Gaza inda ya yi kira ga ɗaukar matakan ƙasa da ƙasa masu ƙarfi, yayin da jaddada buƙatar yin garambawul ga tsarin dokokin duniya na yanzu.
Haka kuma, Erdogan ya jaddada daɗaɗɗen kiransa game da buƙatar yin sauye-sauye a tsarin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya ce “Duniya ta fi ƙarfin tsarin ƙasashe biyar.”
Daga Gaza zuwa ga shugabancin duniya
A cewar fadar shugaban ƙasar, littafin ya kuma ƙunshi batutuwan rikicin da ya shafi Iran, da al’amuran da ke faruwa a Lebanon, da kuma yaƙin Rasha da Ukraine.
Baya ga rikice-rikicen siyasa na yankuna, littafin ya kuma tattauna batutuwan ta’addanci da matsalar sauyin yanayi, da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI), tare da gabatar da ra’ayoyin Erdogan kan yadda tsarin dokokin duniya zai iya zama mai inganci wajen tunkarar ƙalubalen ƙasa da ƙasa.
Fadar shugaban ƙasar ta bayyana littafin a matsayin tushen bayanai ga al’ummar duniya da kuma al’ummar gaba, inda aka fassara shi zuwa harsuna uku domin baiwa mutane da yawa damar fahimtar sakonnin jawabin kan zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma wadata.
Littafin ya kammala da baitunan waƙar baka ta Sezai Karakoc
Littafin ya ƙare da baitukan waƙa ta wani shahararren mawaƙin baka na Turkiyya Sezai Karakoc, wanda ake amfani da kalmominsa wajen jaddada batutuwan gaskiya, da tarihi, da kuma ɗaukar alhaki.
An fitar da littafin ne a daidai lokacin da shugabannin duniya suka taru a New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, yayin da rikice-rikice a Gaza, da kuma na Ukraine da yankin Gabas ta Tsakiya, da tambayoyi game da makomar tafiyar da harkokin duniya, suka mamaye ajandar taron na ƙasa da ƙasa.
Littafin ya ƙare da wani baitin waƙa daga Karakoc:
Sai dai, idan muka yi shiru, tarihi ba zai yi shiru ba.
Idan tarihi ya yi shiru, gaskiya ba za ta yi shiru ba.
Suna tunanin cewa idan suka kawar da mu, batun zai ɓace.
Sai dai, ko da sun kawar da mu, ba za su tsira daga nadamar da za su yi ba.
Ko da sun tsira daga nadamar, ba za su tsira daga hukuncin tarihi ba.
Ko da sun tsira daga hukuncin tarihi, ba za su tsira daga fushin Allah ba.”















