Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar

Salva Kiir ya ɗauki matakin ne domin kauce wa wani giɓi na tsarin mulki.

Newstimehub

Newstimehub

23 Sep, 2026

b9f0bd58 dc6f 4407 ab53 8df4fb0a1c0a 1790149698746

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasa ranar Talata.

A cikin wasu jerin dokoki da aka bayyana a gidan talbijin na ƙasar (SSBC), Kiir ya naɗa jami’ai na riƙon ƙwarya domin ci gaba da kula da ayyukan gwamnati yayin da ƙasar ke shirin zaɓenta na farko tun bayan da ta samu ‘yancin kai.

Shugaba Kiir ya kuma naɗa gwamnoni na riƙon ƙwarya a jihohi 10 da yankunan mulki uku.

An ɗauki matakin ne domin kauce wa giɓi na tsarin mulki, inda wa’din mulkin gwamnatin riƙon ƙwaryar ke ƙarewa ranar Talata.

Yarjejeniyar zaman lafiya

Yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018, wadda ɓangarorin da ke yaƙi suka rattaba wa hannu domin kawo ƙarshen rikicin ƙasar, ta buƙaci gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙarƙare watanni uku gabanin zaɓuka.

Rikice-rikice a Sudan ta Kudu tsakanin shekarar 2013 da 2016 sun haddasa tsundumar ƙasar cikin yaƙin basasa jim kaɗan bayan ta samu ‘yancin kanta a shekarar 2011.

An fara yaƙi a Juba a watan Disambar shekarar 2013 bayan Shugaba Kiir ya zargi korarren tsohon mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar da kitsa juyin mulki. Machar ya musanta zargin.

Sudan ta Kudu za ta yi zaɓukan gama-gari ranar 22 ga watan Disamba, duk da cewan an jinkirta shirye-shiryen zaɓukan kuma rashin jituwa na siyasa game da tsarin zaɓen ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Lokaci gabanin sauyin gwamnati

An kafa Gwamnatin Haɗin kan ƙasa da aka farfaɗo da ita ne ranar 22 ga watan Fabrairun shekarar 2020 bayan rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiyar da aka Farfaɗo da Ita ta shekarar 2018. Yarjejeniyar ta ba da lokaci na sauyi na watanni 36 bayan wani lokaci na watanni takwas gabanin sauyin gwamnati.

A watan Satumbar shekarar 2024, ɓangarorin gwamnatin bisa tanade-tanaden sashe na 8.4 na yarjejeniyar, sun tsawaita lokacin sauyin gwamnatin da watanni 24, daga ranar 22 ga watan Fabrairun 2025 zuwa 22 ga watan Fabrairun 2027. Sun kuma sake canza zaɓukan zuwa watan Disambar shekarar 2026.

Daga baya ne Majalisar Dokoki ta Hadin Kan ƙasa ta amince da tsawaita lokacin kuma Shugaban Jamhuriyar Sudan ta Kudu ya rattaɓa hannu a kai.