Gwamnatin Ghana ta yi watsi da gudunmawar cedi miliyan 20 daga kamfanin MTN

Koda yake gwamnatin ta yaba wa MTN saboda wannan tsari da ‘kyakkyawar niyya,’ ta bayyana cewa gwamnati ta ƙi karaɓr kuɗin ne saboda ta riga ta fitar da isassun kuɗaɗen gudanar da aikin kwashe ‘yanƙasar da kuma sake tallafa wa gina rayuwarsu a gida.

Newstimehub

Newstimehub

26 Aug, 2026

e8ad8878 66f1 478d a686 9c2991a07a35 1780386008618 main

Gwamnatin Ghana ta yi watsi da tayin tallafin kuɗi har cedi miliyan 20 daga kamfanin sadarwa na MTN Ghana, wanda kamfanin ke shirin bayarwa domin tallafawa ‘yan kasar da hare-haren ƙyamar baƙi suka shafa a Afirka ta Kudu. 

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta fitar a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, ma’aikatar ta bayyana cewa ta lura da rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke ambaton Shugaban Hukumar Gudanarwa ta MTN Ghana, Dr. Ishmael Yamson, game da aniyar kamfanin na samar da wannan tallafi. 

Dalilin kin karɓar tallafin

Koda yake ma’aikatar ta yaba wa kamfanin na MTN saboda wannan tsari da kyakkyawar niyya, ta bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar ƙin karaɓr kuɗin ne saboda ta riga ta fitar da isassun kuɗaɗen gudanar da aikin kwashe ‘yanƙasar da kuma sake tallafa musu don gina subuwar rayuwa a gida. 

Sanarwar ta ƙara da cewa, Ministan Harkokin Waje, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya riga ya sanar da Shugaban Hukumar Gudanarwa da Shugaban Hukumar Zartarwa na kamfanin tun a ranar 14 ga Agustan 2026, inda ya sanar musu da matsayar gwamnatin baki-da-baki.

Alƙawarin yin gaskiya da riƙon amana

Ma’aikatar ta tabbatar wa al’umma cewa gwamnati tana kan bakanta na kwaso dukkan ‘yan Ghana da ke cikin haɗari tare da ɗaukar nauyin sake ginawa da daidaita rayuwarsu. 

Bugu da kari, ta yi alƙawarin cewa da zarar an kammala aikin dawo da ‘yanƙasar gida baki ɗaya, ma’aikatar za ta wallafa cikakken bayani kan duk kuɗaɗen da aka kashe a aikin domin tabbatar da gaskiya da rike amana, da amfani da kuɗaɗen jama’a ta hanyar da ta dace. 

Sanarwar ta jaddada cewa ƙasar za ta ci gaba da kasancewa waje mai kyau ga harkokin kasuwanci ga dukkan kamfanonin ƙasashen waje da ke gudanar da sana’o’i a ƙasar, ba tare da la’akari da inda suka fito ba.