Wasu ‘yanta’adda da ake zargi Lakurawa ne sun kashe kusan mutane 30 a lokacin Sallar Jumma’a a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya a makon jiya, kamar yadda majiyoyi a yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Wannan shi ne hari na baya bayan nan da ‘yanta’adda suka kai a Jihar Sokoto.
Shamsuddeen Mai Akwai, sakataren majalisar ƙaramar hukumar Kebbe a ranar Litinin ya ce ana zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne suka kai hari a yankin nasu.
Mai Akwai ya ce maharan na ɗauke da “makamai na zamani” kuma sun kai hari ƙauyen Ungushi “a lokacin da mutane suke tsaka da Sallar Jumma’a.”
Wani mazaunin garin Kebbe da ke kusa, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsaron lafiyarsa, ya ce hare-haren sun biyo bayan kashe sojoji huɗu a Kebbe, shi ma a ranar Jumma’a.
Ya ce an kashe kusan mutane 30 a Ungushi.
Wani mai magana da yawun ‘yansanda ya ce adadin waɗanda aka kashe ya kai 28.















