gabaWata kotun manyan laifuka a Damaskus ta yanke wa tsohon shugaban Syria, Bashar al-Assad, da kaninsa Maher hukuncin kisa a bayan idonsu, bayan samunsu da laifukan cin zarafin bil’adama da wasu laifuka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na SANA ya rawaito.
Kotun Lta Huɗu Mai Shar’ar Manyan Laifuka ta kuma yanke wa ɗan’uwan Assad, Atef Najib, Tsohon Shugaban Reshen Tsaro na Bangaren Siyasa a Daraa, da sauran mutane shida da suka tsare — Fahd Jassem al-Freij da Mohammed Ayman Ayoush da Louay al-Ali da Qusai Ibrahim Mhayoub da Wafiq Saleh Nasser da kuma Talal Fares al-Asimi — hukuncin kisa a ranar Talata.
Mai Shar’a Fakhr al-Din al Aryan ya ce rawar da Assad ya taka wajen aikata laifukan ita ce, ‘matsayi mafi girma ta yanke shawara’, inda ya kara da cewa ya yi amfani da hukumomin gwamnati wajen sauƙaƙa aikata su.
Kotun ta samu Assad da laifin kisan gilla na mutane da dama, ciki har da yara, da azabtarwa, da tsare mutane ba tare da hujja ba da cin zarafin ‘yan’adam, sannan ta yanke masa hukuncin kisa a bayan idonsa.
Kotun ta kuma samu Najib, wanda yake tsare, da laifukan cin zarafin bil’adam, ta kuma yanke masa hukuncin kisa, yayin da aka same Maher al-Assad da sauran mutane shida da ake nema ruwa-a-jallo da laifukan kisan gilla, da azabtarwa da suka yi sanadiyyar mutuwa, da laifukan cin zarafin ‘yan’adam, in ji SANA.
Hukumar ta ce kotun ta nemi a gurfanar da wadannan mutane takwas da ba sa ƙasar a kotunan duniya, kuma ta umarci a fitar da sammacin kama su na ƙasa da ƙasa, in ji SANA.
An gabatar da hukuncin ne a zaman na tara na shari’ar a gaban babban lauyan ƙasar Syria, shugaban Kwamitin Shari’ar Wucin Gadi na ƙasa, wakilan kungiyoyin shari’a da na kare hakkin bil’adama na ƙasa da ƙasa, da ‘yan uwa na waɗanda abin ya shafa.
‘Ba ƙarshen magana ke nan ba’
A martanin farko na cikin gida game da hukuncin, shugaban Kwamitin Shari’ar Wucin Gadi na Kasa, Abdul Basit Abdul Latif, ya bayyana hukuncin a matsayin ‘muhimmin mataki wajen neman adalci, da dawo da hakkokin wadanda abin ya shafa da tabbatar da cewa babu wanda ya i ƙarfin doka’.
‘Wannan ba ita ce ƙarshen magana ba, amma muhimmin mataki ne a kan hanyar neman adalci, dawo da hakkokin wadanda abin ya shafa da tabbatar da doka da oda,’ Abdul Latif ya rubuta a X.
Hukuncin ya zama na farko da kotun Syria ta yanke wa Bashar al-Assad tun bayan kifar da shi daga mulki.
Assad ya gaji mahaifinsa, Hafez al-Assad, a shekara ta 2000 kuma ya mulki Syria kusan shekaru 25 kafin ya gudu zuwa Rasha a ranar 8 ga Disamba, 2024, wanda ya kawo karshen sama da shekaru 50 na mulkin jam’iyyar Ba’ath da ya fara a 1963. Wata gwamnatin wucin-gadi karkashin shugabancin shugaban kasa Ahmad al-Sharaa ta karɓi mulki a Janairu 2025.
Shari’ar ta mayar da hankali ne kan laifukan da manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Syria suka aikata, ciki har da Najib, wanda ya shugabanci reshen Tsaron Siyasa a Daraa.
A lokacin mulkin Assad, gwamnatinsa ta sha zargi daga Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na duniya da gwamnatocin ƙasashen yamma kan aikata laifuka masu yawa, ciki har da kisan jama’a, da azabtarwa, da tsare mutane ba tare da hujja ba, ɓacewa da aka tilasta, da hare-hare kan fararen hula da kayayyakin more rayuwarsu, da kuma amfani da makamai masu guba.
Bayan kifar da Assad, hukumomin wucin-gadi na Syria sun kafa hanyoyin neman alhaki da shari’ar wucin-gadi don bincika laifukan da aka aikata a ƙarƙashin tsohuwar gwamnati, wanda ya sa hukuncin na ranar Talata ya zama muhimmin mataki na shari’a a wannan tsari zuwa yanzu.















