Hukumomin Libya da ke Benghazi sun kori baƙin-haure aƙalla 117,350 na ƙasashe daban-daban waɗanda ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, yayin da ‘yan Sudan fiye da 100,000 suka yi rajista a shirin komawa ƙasarsu don raɗin kansu, kamar yadda gwamnatin da ke kula da gabashi da mafi yawancin kudancin Libya, wadda Majalisar Wakilai ta naɗa, ta bayyana a ranar Litinin.
Shugaban gwamnatin, Osama Hammad, ya bayyana ƙaura ba bisa ƙa’ida ba a matsayin batun da ya shafi ikon ƙasa da tsaro, yana mai kira da a ƙara tsaurara tsaron iyakoki, a ɗauki matakai masu ƙarfi kan ƙungiyoyin safarar mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin gwamnati, a cewar wata sanarwa.
Sanarwar ta ce an riga an fara jigilar ‘yan Sudan da suka yi rajista a shirin komawa gida don raɗin kansu ta jiragen sama na jinƙai.
Haka kuma, gwamnatin ta sanar da wasu sabbin matakai game da ƙaura, ciki har da ƙara tsaurara tsaron iyakoki, sabbin ƙa’idojin zama ga ‘yan ƙasashen waje, tsawaita wa’adin da aka bai wa ma’aikatan ƙasashen waje su daidaita takardunsu zuwa ƙarshen shekarar 2026, da kuma faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kan shirye-shiryen komawa gida don raɗin kai.
Matakan sun kuma haɗa da korar duk wani baƙon da hukumomin tsaro suka hana zama ko kuma wanda aka tabbatar yana ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa, inganta wuraren zama na ma’aikatan baƙi marasa iyali, da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe maƙwabta domin daƙile ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Har yanzu Libya na da gwamnatoci biyu masu hamayya: Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa da duniya ta amince da ita ƙarƙashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibeh, mai hedkwata a Tripoli, wadda ke kula da yammacin Libya; da kuma gwamnatin da majalisar dokokin ƙasar ta naɗa a farkon shekarar 2022, wadda Osama Hammad ke jagoranta kuma ke da hedikwata a Benghazi, wadda ke kula da gabashi da mafi yawan kudancin ƙasar.
Shekaru da dama kenan Ofishin Tallafawa na Majalisar Ɗinkin Duniya a Libya (UNSMIL) ke jagorantar ƙoƙarin cim ma matsaya ta siyasa da za ta kai ga gudanar da zaɓe, wanda ‘yan Libya ke fatan zai kawo ƙarshen rikice-rikicen siyasa da na makamai tare da kawo ƙarshen matakan riƙon ƙwarya da suka ci gaba tun bayan hambarar da Muammar Gaddafi a shekarar 2011.















