An gurfanar da ƙarin mutum 17 bayan tuhumar 33 bisa zargin kisan Malamar Islamiyya a Kaduna

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga Yuni, 2026.

Newstimehub

Newstimehub

27 Jun, 2026

1782558122836 o30p7 46be6a95a8605745d5543cc49d737d7ce5b73043e37fe8868cd4854de1e181a2

Rundunar ’Yansandan Nijeriya reshen Jihar Kaduna ta ce ta kama tare da gurfanar da wasu karin mutane 17 da ake zargi da hannu a kisan wata mata a Maraban Jos, inda ta bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga Yuni, 2026.

Rundunar ta kuma bayyana cewa, bayan kammala binciken wucin-gadi, an tuhumi wasu mutane 33 da laifin haɗa baki wajen aikata laifi da kuma taruwa ba bisa ka’ida ba dangane da lamarin.

A cewar sanarwar, an kuma saki mutane 30 da aka kama tun da farko ba tare da wani sharadi ba, bayan bincike ya tabbatar ba su da hannu a cikin laifin.

’Yan sanda sun ce an ƙara ƙaimi wajen ganowa da kuma kama duk wanda ya shiga ko ya taimaka wajen aikata laifin, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

“Rundunar na sake jaddada cewa bincike na ci gaba. Muna ƙara ƙoƙari wajen ganowa da kama duk wanda ya shiga ko ya taimaka wajen aikata wannan mummunan laifi. Duk wanda aka tabbatar da laifi zai fuskanci hukunci,” in ji sanarwar.

Kwamishinan ’yansanda na jihar, Muhammad Rabiu, ya sake tabbatar da aniyar rundunar ta tabbatar da adalci ga wadda aka kashe da kuma tabbatar da doka da oda a faɗin jihar Kaduna.

Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su zauna lafiya, su bi doka, tare da ci gaba da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wa binciken da ake gudanarwa.

Kisan Malama Ummulkhairi, wata malamar addinin Musulunci, wanda aka yi bisa zargin satar yara a Maraban Jos, ya jawo ce-ce-ku-ce daga hukumomin tsaro, ƙungiyoyin fararen-hula da shugabannin al’umma, inda suka bayyana shi a matsayin mummunan kisan gungun mutane da ya saɓa doka.