Turkiyya za ta aika da jiragen sama na soji biyu dauke da ƙungiyoyin bincike da ceto da kuma ma’aikatan agaji zuwa Venezuela a ranar Juma’a bayan mummunar tagwayen girgizar kasa da suka afka wa yankin Yaracuy, in ji Shugaban Hukumar Kula da Bala’o’i da kai daukin Gaggawa na kasar (AFAD).
AFAD ta ce shirye-shirye sun fara ne bayan samun rahotannin girgizar kasar, inda ta samu haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Waje, da Ma’aikatar Tsaro ta Kasa, da Ma’aikatar Lafiya da kuma tawaga daban ofishin Babban Daraktan Harkokin Tsaro na Fadar Shugaban ƙasa.
Bayan tattaunawa da Babban jami’in tsaron Turkiyya, an ba da izini ga jirgin jigilar sojoji na A-400M don daukar tawagar bincike da ceto da agajin jinƙai ta AFAD mai mambobi 38 daga Istanbul, Izmir da Denizli zuwa Venezuela.
Kazalika jirgin zai dauƙi tawagar ma’aikatan agaji na lafiya ta ƙasa mai mambobi biyar da na kungiyar agajin jinƙai ta Red Crescent ta Turkiyya mai mambobi biyu, da karnukan bincike guda biyu da motocin bincike da ceto guda uku masu cikakken kayan aiki, in ji AFAD.
Haka kuma Ma’aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta ba da izinin sake tura wani jirgin saman soji na biyu ƙirar A-400M dauke da tawagar rundunar agajin jinƙai mai mambobi 22 tare da kayan aikinta, a cewar sanarwar.
An shirya tashin jiragen biyu daga filin jirgin sama na Istanbul Ataturk da misalin karfe 11:15 na safe agogon kasar wato (08:15 GMT) a ranar Juma’a, in ji AFAD.
Ta ce ana sa ido kan halin da ake ciki tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Waje da Ofishin Jakadancin Turkiyya da ke Venezuela.















