Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus a ranar Asabar ya sauka a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC), wajen da Ebola ta fi kamari, in ji wani dan jaridar AFP da ya gane wa idanunusa.
Shugaban ya shaida wa ‘yan jarida a Bunia, babban birnin lardin Ituri, cewa al’ummar duniya na taimaka wa gwamnatin DRC wajen yaki da cutar, amma “a lokaci guda, gudunmawar al’umma tana da muhimmanci’.
Ya ce wannan ne dalilin ziyararsa: “Mun zo ne don tattaunawa da al’umma, don ganin yadda al’amura ke gudana kuma ko akwai matsaloli da za mu iya taimakawa”.
Akwai wannan mummunar cutar mai sa zubar jini da saurin yaduwa a yanzu haka a cikin larduna uku na gabashin DRC da kuma a makwabciyar ƙasar Uganda, inda aka tabbatar da mutum tara sun, ciki har da mutum ɗaya da ya mutu.
Akwai akalla mutum 1,077 da ake zaton sun kamu da Ebola a Congo DRC tun bayan da aka ayyana cutar a ranar 15 Mayu, ciki har da mutuwar mutane 246, in ji Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) a ranar Alhamis.
WHO ta yi gargaɗi cewa yawan waɗanda suka kamu da cutar a DRC zai iya zarta haka, saboda ana ganin ta fara yaduwa kafin a gano ta.
Mafi yawancin ƙasar ta gabashin Afirka — yankin da ya shafe shakaru fiye da shekaru 30 yana fama da talauci da yake-yake — ba shi da isasshiyar damar gudanar da gwaje-gwajen dakunan bincike don tabbatar da waɗanda suka kamu da cutar.
Rikici da Ebola
Uganda ta rufe kan iyakarta da DRC a wannan makon kuma ta ba da umarnin killace duk wanda da ya zo daga wannan ƙasa tsawon kwanaki 21.
A ranar Juma’a, WHO ta sanar cewa wani majinyaci ya warke a ranar Laraba, an sallame kuma ya bar asibiti ya koma cikin al’umma bayan gwaje-gwaje biyu da suka nuna ba shi da cutar.
Anais Legand na WHO ta shaida wa ‘yan jarida a Geneva cewa wannan shi ne “na farko’ daga cikin marasa lafiya da aka tabbatar suna ɗauke da Ebola a wannan cutar.”
Ebola, wadda ke yaduwa ta hanyar kusantar juna da taba ruwan jiki, ta kashe fiye da mutane 15,000 a Afirka cikin shekaru 50 da suka gabata.
Annobar da ta fi kowacce muni a DRC ta yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 2,300 daga cikin 3,500 da suka kamu tsakanin 2018 da 2020.
Kungiyar agaji ta likitoci Doctors Without Borders (MSF) ta fada a cikin wata sanarwa kan sabuwar barkewar cutar cewa “ba a taba samun yawan wadanda suka kamu da Ebola a kwanaki biyar na farkon bayyanarta kamar a wannan karon ba.”
Ta ce adadin kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da ake tura wa yankin har yanzu bai isa ba.
Ayyukan gwamnati a yawancin bangarorin lardin Ituri ba su da yawa, inda samun damar zuwa wurare ke da wahala saboda rashin tsaro kasancewar mayakan ADF da ake danganta su da IS da sauran kungiyoyin ‘yan bindiga da ke yawan kashe fararen hula.
Lardunan Kivu ta Arewa da Kudu da ke kusa, wadanda su ma aka ga samu barkewar cutar, sun sha fama da tashin hankali na kusan shekaru talatin.
Manyan sassan yankin suna hannun kungiyar M23 mai samun goyon bayan Rwanda, wadda ke yaki da sojojin gwamnati.
Miliyoyin mutane sun guje wa yakin, kuma suna rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fama da rashin tsafta.
Kusan mutum miliyan daya daga cikin ‘yan gudun hijira na zaune a lardin Ituri, inda damuwar cewa annobar za ta yadu cikin sansanonin ya tayar da hankali.
Dorcas Mapenzi ta fada a sansanin Kingonze a kusa da Bunia: “Idan Ebola ta zo, za a shafe mu gaba ɗaya domin muna matuƙar cunkushe kamar sardine”.
Babu rigakafi ko magani na musamman don nau’in Ebola na Bundibugyo, wanda ke hiafar da wannan cutar.
Amma shugaban CDC na Afirka ya faɗa a ranar Alhamis cewa ana sa ran samun rigakafin kafin ƙarshen shekarar nan.














