Erdogan ya yi bikin cika shekaru 573 da ƙwace Istanbul, ya yi jinina ga Mehmed II

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce nasarar da a aka samu a 1453 ta kawo zaman lafiya, da tsaro, da sabunta birnin, inda ya kira shi matsayin lokacin da ya sauya tarihi.

Newstimehub

Newstimehub

30 May, 2026

a5f271a1 da5c 477a 8391 47d7f0fb7019 1780077055335

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi bikin cika shekaru 573 da mamayar da Daular Usmaniyya ta wa Istanbul, yana bayyana wannan lamari ba wai kawai a matsayin babbar nasarar soja ba ce, amma a matsayin wani sauyi da ya kawo zaman lafiya, tsaro, da sabunta birnin.

Yayin jawabi a shirin “Daga Mamayar Istanbul zuwa Mallakar Zuciya” da reshen jam’iyyar Adalci da Ci Gaba (AK) na lardin Istanbul ya shirya a ɗakin taro na Halic Congress Center ranar Juma’a, Erdogan ya yi jinjina wa waɗanda suka bayar da gudunawa a mamayar ta 1453, ƙarƙashin jagorancin Sultan Mehmed II, wanda ake kira (Ci-gari) Fatih Sultan Mehmet.

“A wannan rana mai girma, cikin tausayawa ina tunawa da dukkan manyanmu da suka halarci mamayar Istanbul shekaru 573 da suka wuce, da waɗanda suka yi shahada ko suka tsira suka zama tsoffin sojoji a cikin ganuwar birnin,” in ji Erdogan.

“Haka kuma ina girmama tunawa da wannan babban kwamandan da ya ƙwace Istanbul yana da shekaru 21. Allah ya sa cikar shekaru 573 na mamayar ta kasance albarka da sa’a.”

Erdogan ya ce mamayar “ba kawai babbar nasara ba ce” ko wani lamari da “ya buɗe kuma ya rufe wani zamani ba,” amma “juya duhu ne zuwa haske a ɗaya daga cikin biranen duniya da aka fi ƙauna.”

Ya ce lamari ya samar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa, ta hanya karfafa haƙuri da mutane masu asali da aƙidu mabambanta, kuma ya farfaɗo da birni da ya doshi durƙushewa.

Istanbul: Tauraruwar Turkiyya

Yayin da ya ke maganar masanin tarihi marigayi Halil Inalcik, Erdogan ya ce Sultan Mehmed II ya yi aiki ba dare ba rana don cim ma mamayar sannan daga baya ya sake gina Constantinople ya zama babban birni na Musulunci na Turkiyya ta hanyar gidauniyoyi da cibiyoyin gwamnati.

Erdogan ya kuma ambaci wata magana ta Annabi SAW da ake dangatawa da mamayar Constantinople: “Tabbas za a kwace Constantinople. Madalla da kwamandan zai kasance wanda ya ƙwace ta, kuma madalla da rundunar sojin da za ta kasance wannan runduna.”

Ya bayyana mamayar a matsayin mafi haske a cikin jerin nasarori da suka faro tun daga yakin Manzikert a 1071 kuma ya ce ta nuna abin da ƙasar Turkiyya za ta iya cim mawa yayin da take neman cikar burinta.

Dangane da shahararren al’amari inda aka kai jiragen ruwa na rundunar Usmaniyya ta kan ƙasa zuwa cikin ruwan da ake cewa mashiga zinari, Golden Horn, Erdogan ya ce wannan aikin ya nuna karsashin Sultan Mehmed da bangaskiyarsa ga nasara.

Ya ce tun daga 1453, Istanbul ta kasance “tauraruwa ta ƙasa” kuma ya soke waɗanda a ra’ayinsa, har yanzu ke adawa da nasarorin mamayar. Ya yi iƙirarin cewa kiran sauya matsayin Istanbul ko suka ga tarihin birnin suna nuna yadda har yanzu ba a warware taƙaddama kan mamayar da abin da ta wanzar ba.

Shugaban ƙasa ya ce Turkiyya za ta ci gaba da kiyaye Istanbul a matsayin wani abin da Fatih Sultan Mehmet ya gadar, kuma za ta cim ma nasarori a nan gaba ta hanyar la’akari da mamayar.

“Idan muka gaskata sosai, muka yi aiki, muka jurewa wahalhalu, babu wani aiki da ba za mu iya yi ba kuma babu wani buri da ba za mu iya cikawa ba,” in ji shi, yana tunasar da shahararriyar azamar Sultan Mehmed ta kwace birnin.