Rahoto ya bayyana cewa Saudiyya ta kai wasu hare-hare da dama a ɓoye kan Iran a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da aka kai mata a cikin masarautar yayin yakin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wasu jami’an yammacin duniya biyu da kuma jami’an Iran biyu suka shaida.
Rahoton ya ce waɗannan hare-hare na Saudiyya, da ba a taɓa bayyana su a baya ba, su ne karon farko da aka tabbatar cewa masarautar ta kai farmaki kai tsaye a ƙasar Iran.
Wannan kuma ya nuna cewa Riyadh na ƙara ƙarfafa matsayinta wajen kare kanta daga babbar abokin hamayyarta a yankin.
Jami’an sun ce an kai harin ne da jiragen yaƙi na sojin saman Saudiyya a ƙarshen watan Maris, inda ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa “ramuwar gayya ce bisa hare-haren da aka kai wa Saudiyya.”
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce bai samu tabbacin takamaiman wuraren da aka kai harin ba.
A martanin da ya bayar, wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya bai tabbatar ko ya musanta faruwar hare-haren ba. Haka kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran ba ta mayar da martani ba kan bukatar jin ta.
Rahoton ya ce Saudiyya, wadda ke da alaƙar soja mai ƙarfi da Amurka, ta dade tana dogaro da kariyar sojojin Amurka, amma yakin da ya ɗauki makonni 10 ya bar masarautar cikin yanayin rauni, inda kariyar Amurkar bai hana kai mata hare-hare ba.
Kasashen Gulf sun fara mayar da martani
Rahoton ya nuna cewa wannan rikici na kara faɗaɗa, inda yakin da ya fara bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai Iran a ranar 28 ga Fabrairu ya jawo sauran ƙasashen Gabas ta Tsakiya cikin rikicin ta hanyoyin da ba a bayyana a fili ba.
Tun bayan wadannan hare-hare, Iran ta kai hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan dukkan ƙasashen Hadaddiyar Ƙungiyar Kasashen Gulf (GCC), inda ta kai hari ba kawai sansanonin sojojin Amurka ba, har ma da wuraren fararen-hula, filayen jirgin sama da cibiyoyin mai, tare da rufe Mashigar Ruwan Hormuz wanda ke shafar kasuwancin duniya.
Rahoton ya kuma ce Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ita ma ta kai hare-haren soja kan Iran, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito.
Wannan ya nuna cewa ƙasashen Gulf sun fara mayar da martani a ɓoye kan Iran bayan hare-harenta.
Sai dai rahoton ya ce dabarun ƙasashen biyu sun bambanta, inda UAE ke nuna matsaya mai tsauri wajen mayar da martani, yayin da Saudiyya ke ƙoƙarin rage tashin hankali tare da ci gaba da tattaunawa da Iran.
Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ya ce masarautar na ci gaba da matsayarta na neman zaman lafiya da rage tashin hankali domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.














