Fitaccen ɗan gudun Kenya, Sabastian Sawe, ya samu gagarumar tarba a gida bayan ya kafa tarihi a gasar London Marathon, inda ya zama na farko da aka amince da shi da karya shingen awa biyu. An tarbe shi ne a filin jirgin saman Jomo Kenyatta International Airport da girmamawa ta musamman, tare da ruwan ban girma, rawa ta gargajiya da halartar jami’ai ciki har da ministan wasanni Salim Mvurya.
Bikin ya ci gaba a wani taro na musamman karkashin jagorancin shugaban ƙasa William Ruto, wanda ya bayyana nasarar Sawe a matsayin wani babban lokaci a tarihin juriyar dan Adam. Shugaban ya ba shi kyautar kusan dala 61,000 tare da mota domin karrama wannan gagarumar nasara.
Sawe ya lashe tseren ne da lokaci na 1:59:30, inda ya karya tarihin da ya gabata da dakika 65. Haka kuma ya bai wa shugaban ƙasa takalman da ya yi amfani da su a tseren tare da hoton da aka sa hannu don tunawa da wannan tarihi.
Duk da wannan shahara, Sawe ya nuna tawali’u, yana mai cewa yana alfahari da abin da ya cimma kuma yana tunanin yadda zai kara inganta wannan rikodi. Iyalan sa ma sun bayyana yadda tun yana karami yake nuna kwarewa, inda mahaifiyarsa ta ce tun yana yaro yake gudu da sauri har sun san zai zama babban ɗan wasa.
Wannan nasara ta Sawe ta zama abin alfahari ga Kenya, tare da kara haskaka tarihin kasar wajen gudun nesa da kuma zama alamar nasarar kasa baki daya.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB














