Attajirin duniya Elon Musk ya bayyana a gaban kotu cewa shi ne ya kirkiri ra’ayin OpenAI tun farko, amma daga baya shugabanninta sun karkatar da manufarsa. A cikin shari’ar da ake yi kan makomar kamfanin, Musk ya zargi Sam Altman da Greg Brockman da cin amanarsa da kuma sauya OpenAI daga ƙungiya mai zaman kanta zuwa wacce ke neman riba.
Musk ya ce manufar farko ita ce a samar da fasahar AI domin amfanin bil’adama ba tare da anfani na kai tsaye ga wasu mutane ba. Ya kara da cewa shi ne ya kawo ra’ayin, ya tara manyan ma’aikata, ya koyar da su, kuma ya bayar da kudaden farko. Ya gargadi cewa idan aka bar ƙungiyoyin agaji ana amfani da su wajen neman riba, hakan zai iya lalata tsarin bayar da tallafi gaba ɗaya.
Sai dai lauyoyin OpenAI sun musanta zargin, suna cewa Musk ne tun farko yake son a mayar da kamfanin zuwa na riba domin ya samu iko a kansa. Lauyan su, William Savitt, ya ce Musk ya fara wannan shari’a ne bayan ya kasa cimma burinsa, yana mai cewa abin da yake nema shi ne ya kasance a saman iko. A shekarar 2023 ma, Musk ya kafa nasa kamfanin AI mai suna xAI.
A bangaren Musk kuma, lauyansa Steven Molo ya ce OpenAI ce ta karkata zuwa son kuɗi, musamman bayan ta fara samun manyan masu zuba jari ciki har da Microsoft. Ana sa ran Musk zai ci gaba da bayar da shaida yayin da shari’ar ke gudana, wacce za ta iya shafar makomar OpenAI da kuma yadda ake tafiyar da fasahar AI a duniya.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB










