Türkiye ta bayyana damuwarta cewa rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran na iya bazuwa zuwa dukkan yankin Gabas ta Tsakiya. Ma’aikatar Tsaron ƙasar ta ce hare-haren da ake ci gaba da kaiwa Iran da kuma martanin da ake samu sun ƙara haddasa haɗarin rikidewar rikicin zuwa babban yaƙin yanki.
Kakakin ma’aikatar, Zeki Aktürk, ya jaddada cewa dole ne a warware duk wata takaddama ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya, bisa dokokin ƙasa da ƙasa. Ya ce Türkiye na ci gaba da tsayawa kan wannan matsaya, tare da fatan ganin an kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Haka kuma, Aktürk ya soki ayyukan soji na Isra’ila a wurare da dama ciki har da Lebanon, Syria da yankunan Falasdinu. Ya ce waɗannan hare-hare sun saba dokokin ƙasa da ƙasa da na jin ƙai, yana mai nuni da cewa har ma wasu sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun rasa rayukansu a Lebanon.
Ya kuma yi zargin cewa Isra’ila na ci gaba da keta ikon Syria ta hanyar hare-hare a kudancin ƙasar, tare da cigaba da ayyukan gine-ginen matsugunan da ba su halatta ba a Yammacin Kogin Jordan da kuma hare-hare a Gaza.
A ƙarshe, Türkiye ta yi kira ga ƙasashen duniya, musamman Majalisar Dinkin Duniya, da su ɗauki matakai domin dakatar da wannan rikici, tana mai gargadin cewa rashin daukar mataki zai ƙara raunana amincewa da tsarin dokokin ƙasa da ƙasa.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB














