Shugaban ƙasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na tafiyar da rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya cikin taka-tsantsan, tare da kiyaye dangantakar makwabtaka da ’yan’uwa. Ya jaddada cewa Türkiye ba za ta fada cikin “tarkuna” da ake shimfiɗa mata ba, kuma tana da niyyar nisantar abin da ya kira “zoben wuta” a yankin.
Erdogan ya ce rikicin da ke faruwa ba ya shafar ƙasa ɗaya kawai, yana jawo illa ga duniya baki ɗaya. Ya zargi Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da jagorantar abin da ya kira “tsarin kashe-kashe”, yana mai cewa dole ne a dakatar da hakan cikin gaggawa domin kare zaman lafiya da mutuncin ɗan Adam.
Ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki mai ƙarfi da jarumta don kare hanyoyin diflomasiyya, yana mai gargadin cewa tsattsauran ra’ayin Isra’ila na iya lalata duk wani yunkuri na warware rikicin ta hanyar tattaunawa.
Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran tun daga ƙarshen watan Fabrairu, wanda Iran ta mayar da martani da hare-haren jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami a yankin. Duk da sanarwar dakatar da wasu hare-hare daga Amurka, Iran ta musanta cewa akwai wata tattaunawa kai tsaye, duk da cewa ta amince da karɓar saƙonni daga wasu ƙasashe abokai.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB














