Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi ikirarin cewa an kashe Ali Larijani da kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani, a wasu hare-haren sama da aka kai cikin dare. A cewarsa, harin ya shafi manyan jami’an tsaron Iran, inda ya bayyana cewa an “kawar” da su a wani farmaki da aka kai.
Sai dai har zuwa yanzu, hukumomin Iran ba su tabbatar da wannan ikirari ba. Maimakon haka, wasu kafofin yada labaran gwamnatin Iran sun wallafa wani rubutu da aka ce daga Larijani ne, lamarin da ke ƙara jefa shakku kan rahoton mutuwarsa.
Rahotanni sun nuna cewa Larijani, wanda ke da matsayi mai girma a harkokin tsaron ƙasa, yana cikin muhimman mutanen Iran, kuma an gan shi kwanan nan a Tehran yayin wani taron jama’a. Idan har aka tabbatar da mutuwarsa, hakan zai zama babban rashi ga shugabancin tsaron Iran.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ke ƙaruwa, yayin da Amurka ma ta sanar da lada mai tsoka ga duk wanda ya bayar da bayanai kan manyan jami’an tsaron Iran da ake nema.









