Sabon tashin hankali a Sudan ta Kudu ya tilasta kimanin mutum 100,000 tserewa zuwa ƙasar Habasha, kamar yadda UNICEF ta bayyana. Rikicin ya fara ne bayan sojojin ƙasar sun bayar da umarnin kwashe jama’a daga garin Akobo a ranar 6 ga Maris, wanda ya zama sabon wurin rikici tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.
Rahotanni sun ce duk da cewa sojoji sun yi ikirarin sun karɓe ikon garin, har yanzu ana fuskantar matsalar rashin tabbas sakamakon ƙarancin sadarwa. Mutane da dama sun tsere zuwa yankuna mafi aminci a cikin ƙasar, yayin da wasu suka tsallaka iyaka zuwa Habasha domin neman mafaka.
Halin jin kai na ƙara taɓarɓarewa, musamman ga yara, inda ake fuskantar ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki. Haka kuma, an rufe asibitin Akobo tare da lalata wasu cibiyoyin lafiya sama da 20, yayin da cutar kwalara ke ci gaba da yaduwa a yankin.
Masu lura da al’amura na ganin wannan rikici na iya jefa ƙasar cikin sabon yaƙin basasa, duk da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 tsakanin shugaba Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar, wanda yanzu alamun rushewarsa ke bayyana.














