Gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da wani hari da jirgin sama marar matuki ya kai a ƙauyen Shukeiri da ke Jihar White Nile, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla fararen hula 17. Hukumomi sun zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF)da kai harin, suna mai cewa lamarin ya faru ne a wannan watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa, Firaminista Kamil Idris da mambobin gwamnatinsa sun bayyana harin a matsayin abin ƙazanta, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu. Gwamnatin ta kuma bukaci al’ummar duniya su ɗauki mataki kan RSF, har ma ta nemi a sanya rundunar cikin jerin ƙungiyoyin ta’addanci.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faɗa kan makarantar sakandare da kuma cibiyar lafiya a ranar Laraba, inda mafi yawan waɗanda suka mutu ‘yan mata ɗalibai ne. Haka kuma kusan mutane 10 sun jikkata. Kungiyar Likitocin Sudan ta ce mamatan sun haɗa da ɗalibai, malamai da kuma wani ma’aikacin lafiya.
Rikicin Sudan ya fara ne tun Afrilun 2023 bayan faɗa tsakanin sojojin gwamnati da RSF, wanda ya jawo mutuwar dubban mutane tare da tilastawa miliyoyin jama’a barin gidajensu.














