An samu cece-kuce a Ghana bayan rahotanni cewa Shugaba John Mahama na amfani da jirgin sama mai zaman kansa na ɗan’uwansa wajen yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje. ‘Yan siyasa daga jam’iyyar adawa ta NPP sun bukaci a gudanar da bincike, inda ɗan majalisa Abdul Kabiru Tiah Mahama ya ce hakan na iya zama saɓawa ƙa’idar aiki ga jami’an gwamnati kuma na iya nuna rikicin anfani.
Sai dai gwamnati ta kare matakin shugaban ƙasar, tana cewa babu wata matsalar rikicin anfani a cikin lamarin. Ministan sadarwa na gwamnati, Felix Ofosu Kwakye, ya shaida wa gidan rediyon Joy FM cewa amfani da jirgin ɗan’uwan shugaban na taimakawa rage kuɗin gwamnati, domin gwamnati tana biyan kuɗin mai da kuɗin saukar jirgi ne kawai.
Duk da haka, ‘yan adawa sun ce wannan bayanin bai gamsar da su ba. Batun ya sake tasowa ne yayin da shugaban ƙasar ke gudanar da wasu tafiye-tafiye zuwa ƙasashe daban-daban, ciki har da Koriya ta Kudu, Habasha domin taron Tarayyar Afirka, da kuma Tanzaniya.
Jirgin shugaban ƙasar Ghana, nau’in Falcon 900EX EASy da aka sayo tun 2009, ya shafe watanni takwas ana gyara shi a Turai kafin a dawo da shi ƙasar a bara. Rahotanni sun ce jirgin ya taɓa samun matsaloli na aiki sau da dama, lamarin da ya sa gwamnati ke cewa amfani da wani jirgi na daban yana da amfani ga tsaro da kuma kuɗin gwamnati.














