Nijar ta yi tir da ‘ɗabi’ar raini’ ta Tarayyar Turai kan ƙudurin neman sakin Bazoum

Ministan harkokin waje da haɗin kai da kula da ‘yan Nijar a ƙetare, Bakary Yaou Sangaré, ya yi sammancin jakadiyar Tarayyar Turai a Nijar, Mrs. Nicoletta Avella, zuwa ofishinsa ranar Alhamis domin nuna fushin gwamnatin ƙasar kan ƙudurin majalisar dokokin Tarayyar Turai kan halin da tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ke ciki. Kamfanin dillancin labaran […]

Newstimehub

Newstimehub

13 Mar, 2026

2d852d73df590ba2424714e9ea20a00226910d466aa36444feb67e4d37da7b92

Ministan harkokin waje da haɗin kai da kula da ‘yan Nijar a ƙetare, Bakary Yaou Sangaré, ya yi sammancin jakadiyar Tarayyar Turai a Nijar, Mrs. Nicoletta Avella, zuwa ofishinsa ranar Alhamis domin nuna fushin gwamnatin ƙasar kan ƙudurin majalisar dokokin Tarayyar Turai kan halin da tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ke ciki.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito cewa bayan ganawarsu, ministan ya miƙa mata wasiƙar koke inda gwamnati Nijar ta yi Allah wadai da tsoma bakin Tarayyar Turai cikin harkokin cikin gidan Nijar.

Gwamnatin Nijar ta yi tir da irin wannan ɗabi’ar raini ta Tarayyar Tutrai, yayin da take bayyana jajircewarta wajen ƙin ɗaukar raini daga ko ina, kamar yaddda kamfanin dillancin labaran ANP ya tuwaito.

Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta gabatar da ƙudurin neman a saki Bazoum ne a wani zaman da ta yi ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2026.

Majalisar ta yi iƙirarin cewa harkar tsaro da jinƙai na taɓarɓarewa a Nijar da ma yankin Sahel, lamarin “ da ya sa kusan mutane miliyan ɗaya suka rabu da gidajensu kuma mutum miliyan uku suna buƙatar agaji, wanda aka taƙaita sosai bayan an soke ƙungiyoyi masu zaman kansu masu yawa tare da korar ma’aikatan ƙetare.”

 Ƙundurin ya ce majalisar “Ta yi Allah wadai da ci gaba da riƙe Shugaba Bazoum da aka zaɓa a tafarkin dimokuraɗiyya da matarsa da kuma sauran mutane da aka kama a juyin mulkin, kuma ta yi kira da sake su nan-take ba tare da sharaɗi ba.”

Kazalika ƙudurin ya yi kira ga ƙungiyar Tarayar Afirka da ƙasashen duniya su ci gaba da mastin lamba kan a saki shugaba Bazoum.

Kana majalisar ta sa a miƙa ƙudurin ga Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Ƙungiyar AES.

Juyin Mulki

Ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 ne aka yi juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, inda Janar Abdourahamane Tiani ya karɓi ragamar mulki.

A wancan lokacin ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi barazanar kai hari domin dawo da Bazoum kan mulki.

Barazanar ta sa ƙasashen Mali da Burkina Faso, inda a nan ma sojoji sun yi juyin mulki, suka ce idan aka kai wa Nijar hari su ma za su rama mata.

Daga nan ne ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka ɓalle daga ƙungiyar ECOWAS inda suka kafa ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel AES.

Daga bisani an ƙara wa shugaban na Nijar girma zuwa muƙamin cikakken Janar na soji a shekarar 2025, kuma taron sake fasalin siyasar ƙasar ya ba shi damar mulki na shekara biyar.

Bayan an rantsar da shi Shugaba Tiani ya yi alƙawarin yin iya ƙoƙarinsa domin yin aiki yadda mutanen ƙasar ke fata.

Tushen labari:Newstime hub