Dan wasan gudu na Uganda, Jacob Kiplimo, ya sake kafa sabon tarihin duniya a gasar half marathon bayan ya lashe tseren da aka gudanar a Lisbon ranar Lahadi da lokaci na mintuna 57 da dakika 20. Wannan nasara ta karya tsohon tarihin da dan wasan Ethiopia Yomif Kejelcha ya kafa a shekarar 2024 da dakika 10. Kiplimo dai shi ne ya rike tarihin a shekarar 2021 kafin Kejelcha ya karya shi da dakika guda a Valencia.
A lokacin tseren, Kiplimo ya fara da gudu cikin sauri inda ya kammala kilomita 5 na farko cikin mintuna 13:28, yayin da ‘yan tseren Kenya Nicholas Kipkorir da Gilbert Kiprotich ke binsa a baya. Sun isa kilomita 10 cikin mintuna 27:00, amma daga baya Kiprotich ya kasa ci gaba da wannan saurin.
Lokacin da suka kai kilomita 15 cikin mintuna 40:52, Kiplimo ya kara sauri sosai, inda ya kammala kilomita 5 na gaba cikin mintuna 13:31 kafin ya kai ga layin ƙarshe. Bayan tseren, Kiplimo ya ce bayan kilomita 10 na farko ya fahimci cewa zai iya karya tarihin duniya, shi ya sa ya kara matsa kaimi a kilomita biyu na ƙarshe. Kipkorir ya zo na biyu da tazarar dakika 48, yayin da Kiprotich ya zo na uku.
A bangaren mata kuma, ‘yar tseren Ethiopia Tsige Gebreselama ta sake kare kambunta bayan ta lashe gasar da lokaci na awa 1 da mintuna 04 da dakika 48.














