Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jimaminsa game da rasuwar fiye da mutum 30 a wani tsarin mota da aka yi a Kwanar Barde a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na gidan gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi ta ambato gwamnan yana bayyana lamarin a matsayin babban rashi ba ga iyalan mamatan kawai ba har ga ɗaukacin jihar.
“Gwamnan ya umarci ma’aikatar kiwon lafiyar jihar ta tabbatar da cewa dukkan waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke asibitoci su sun samu magani kyauta ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji sanarwar.
“Kana ya ba da umarnin cewa ofishin mai ba da shawara na musamman game da harkar jinƙai a jihar ya yi nazari game da waɗanda lamarin ya shafa ya kuma tsara matakan tallafa wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su,” in ji ta.
Kazalika sanarwa ta ce gwamnan ya bai wa masu tuƙin motoci, musamman masu tuƙin manyan motoci, su ƙaurace wa tuƙin ganganci su kuma bi dokokin tuƙi domin kauce wa irin wannan bala’in nan gaba.














