Reshen kungiyar Daesh a yankin Sahel ya bayyana cewa shi ne ya kai harin da aka kai Sansanin Sojin Sama na Nijar wanda ke kusa da filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Diori Hamani a Yamai. Kungiyar ta bayyana hakan ne ta shafin da take yaɗa farfaganda Amaq.
A cikin sanarwar, Daesh ta bayyana harin a matsayin “hari na bazata kuma wanda aka shirya” wanda ya janyo ɓarna mai yawa ga sansanin. Kamfanin SITE Intelligence Group, wanda ke sa ido kan ayyukan kungiyoyin ta’addanci, ya tabbatar da wannan ikirarin. Sai dai, sabanin yadda ƙungiyar ta saba, Daesh ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda aka kai harin ba, kuma ba ta fadi adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.
Tun kafin ikirarin Daesh, hukumomin Nijar sun riga sun tabbatar da cewa an kai harin a daren Laraba, 28 ga Janairu, zuwa safiyar Alhamis, 29 ga Janairun, 2026. A cewar Ministan Tsaron Kasa, maharan ɗauke da makamai sun kai harin ne a kan babura kusan karfe 12:20 na dare. Dakarun Tsaro da Kare Kasa na Nijar (FDS), tare da taimakon abokan haɗin gwiwarsu na Rasha, sun ɗauki matakin gaggawa kuma sun fatattaki maharan bayan kusan mintuna talatin na musayar wuta.
Rundunar sojin ta bayyana cewa an kashe kimanin maharan 20, ciki har da wanda aka bayyana a matsayin ɗan Faransa, yayin da aka kama mutane 11 da rai. An kuma ƙwato makamai, harsasai, babura da sauran kayan aikin soja, kamar yadda hotunan da aka nuna a gidan talabijin na kasa (RTN) suka tabbatar. Ba a samu asarar rai a ɓangaren sojojin Nijar ba, sai dai sojoji huɗu sun jikkata.
A lokacin da suke ja da baya, maharan sun harbi jiragen farar-hula uku da ke tsaye a filin jirgi. An harbi jiragen Asky Airlines biyu da kuma jirgin Air Côte d’Ivoire Airbus A319 guda ɗaya, amma ba a samu asarar rayuka ba. Daga cikin ɓarnar da aka samu akwai ƙonewar wata ma’ajiya ta harsasai.
Sansanin Sojin Sama na Base 101 wuri ne mai matukar muhimmanci. Yana a kudancin birnin Yamai, kuma yana ɗauke da hedikwatar Hadakar Rundunar Tarayyar Afirka (FU-CAES), wanda sansani ne da dakarun haɗin gwiwa na Rasha da Afirka ke amfani da shi da kuma dakarun Italiya waɗanda ke aikin taimako a Nijar. A baya-bayan nan ma, an adana uranium mai yawa a sansanin, a lokacin da ake rikici da kamfanin nukiliya na Faransa wato Orano.









