Ƙungiyar ƙwadago ta direbobin tirelolin dakon mai a Nijeriya (NUPENG) ta yi shelar dakatar da yajin aikinta bayan ta ƙulla yarjejeniya da shugabannin matatar man Dangote kan amincewa da ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiyoyin ƙwadago.
An cim ma yarjejeniyar ne a wata tattaunawar sirri da hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasar (DSS) ta jagoranta kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya suka halarta.
Muƙaddashin sakataren NLC, Benson Upah, ne ya tabbatar da sakamakon tattaunawar yayin da ma’aikatar ƙwadagon Nijeriya ta ce za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba.
An cim ma wannan matsaya ne a tattunawar da ma’aikatar ƙwadagon tarayya ta jagoranta ranar Litinin 8 ga watan Satumba bayan NUPENG tayi barazanar soma yajin aiki kan yadda kamfanin ya ƙi amincewa da ‘yancin ma’aikatansa na shiga ƙungiyar ƙwadago.