‘Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC, sun yi garkuwa da wani ɗan China

Majiyoyi sun ce maharan sun buɗe wuta kan jami’an ne inda suka kashe takwas daga cikinsu nan-take. Sun kama ɗaya daga cikin ‘yan China, yayin da huɗu suka tsallake rijiya da baya.

Newstimehub

Newstimehub

6 Sep, 2025

577048a23bc865d5516d297dd6a99efcf3026e6cb0b68ae2ccff425d93b56d1c

Masu garkuwa da mutane sun kashe jami’an rundunar NSCDC ranar Juma’a da daddare kuma suka kama wani ma’aikaci ɗan ƙasar China a Okpella da ke ƙaramar hukumar Etsako East a Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma jikkata jami’an rundunar NSDC huɗu da kuma wani farar-hula a lokacin harin, kuma ana yi wa waɗanda suka jikkata a wani asibiti.

Jami’an, waɗanda ke aikin tsaro a kamfanin simintin BUA, na kan hanyarsu ta raka ‘yan China biyar zuwa wurin aikinsu a lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna kusa da ƙofar kamfanin, in ji rahotanni.

Majiyoyi sun ce maharan sun buɗe wuta kan jami’an ne inda suka kashe takwas daga cikinsu nan-take. Sun kama ɗaya daga cikin ‘yan China ɗin, yayin da aka kuɓutar da huɗu.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, wani babban jami’i na rundunar NSCDC na Jihar Edo ya ce ma’aikatan suna aikin rakiya ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin da misalin ƙarfe 10:00 na dare.