Shugaba John Dramani Mahama na Ghana ya ce ƙasar ba za ta iya ci gaba da kashe dala miliyan 15 a ko wace shekara domin hayar gidaje da ofisoshin jakadanci ba.
“Hakan ba amfani da kuɗin masu biyan haraji ta hanyar da ta dace ba ne, kuma akwai buƙatar a daina wannan,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato shugaban ƙasar yana cewa.
Shugaba Mahama ya ce wannan shi ya sa majalisar ministocin ƙasar ta amince da shirin STRIDE na dabarun sauyawa daga haya zuwa gina gidajen da ƙasar za ta yi amfani da su a ƙasashen ƙetare.
Shugaban ya bayyana cewa ya bai wa ministocin harkokin waje da na kuɗi aikin warware wannan matsalar da ta daɗe tana damun ƙasar.
Ya ce daga bayanan da aka ba shi a baya bayan nan, ya fahimci cewa an riga an naɗa mai ba da shawara game da kashe kuɗi kuma ana zanen gine-ginen yayin da ake tattaunawa game da yadda za a samu kuɗaɗen gina su.