DSS ta gurfanar da shugabannin Ansaru da ‘ke da alaƙa da fasa gidan yarin Kuje’ da laifin ta’addanci

A cewar hukumar ta sirri, laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.

Newstimehub

Newstimehub

5 Sep, 2025

fe3ace07012ad4c6a144299f629d0e39573ef92235eb3ec8519d8a152f7cba08

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wasu manyan kwamandojin kungiyar Ansaru biyu, wata kungiyar ta’addanci da aka ce suna da alaƙa da Al-Qaeda, kan zarginsu da hannu wajen kai munanan hare-hare a Nijeriya.

Wadanda ake zargin su ne Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas/Mukhtar, wanda aka bayyana a matsayin Sarkin Ansaru, da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda.

An kama su ne a kwanan nan a yayin gudanar da ayyukan tsaro.

A cewar hukumar ta sirri, laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.

Ana zargin mutanen biyu da hannu a harin da aka kai gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, inda fursunoni fiye da 600 da suka hada da wadanda ake zargi da Boko Haram suka tsere.