Tawagar IMF ta kai ziyara Nijar domin ba da taimako na ƙwararru

A watan Mayun da ya gabata wata tawagar IMF ta gana da Firaministan Jamhuriyar Nijar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

4 Sep, 2025

cc82abdf87a990c7e80562fbc56ff9586f3d55757d0e345412bd3f77a510bf3e

Firaminista kuma Ministan Kuɗi na Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Asusun Ba Da Lamuni na IMF da ta kai ziyarar aikin ƙasar Nijar ranar Laraba domin tattaunawa kan harkokin kuɗi da tsimi da tanadi.

Tawagar ta ƙwararru ta kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin Ms. HA VU, babbar masaniyar tattalin arziki a ɓangaren kuɗi da haraji na asusun a IMF.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar, ANP ya ambato wata sanarwa na cewa, “Nijar a matsayinta na mamba a Asusun Ba Da Lamuni na IMF, ta nemi wannan taimakon na ƙwararru daga IMF domin inganta da kuma ƙarfafa ayyukan gwamnati.”