Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello ya ce ba wanda aka kama zuwa yanzu dangane da harin da aka kaiwa ayarin motocin tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami.
CP Bello ya shaidawa manema labarai bayan wani taron tsaro da gwamnan jihar ya yi, cewa lamarin da ya faru a kewayen unguwar GRA, yana da alaƙa da wasu ‘yan daba ne masu alaƙa da wata ƙungiyar siyasa.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, wasu ‘yan siyasa ma suna karya dokar hana amfani da jiniya da kuma yin yaƙin neman zaɓe ba tare da izini ba.
Ya bayyana cewa an samar da matakan tsaro domin tabbatar da bin doka da oda, yayin da ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kwantar da hankalinsu.
Ya jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya.