Turkiye ta sake tabbatar da cikakkiyar dakatar da cinikayya da Isra’ila, inda Ministan Harkokin Waje ya sanar da cewa jiragen ruwa na Turkiyya ba za su sake samun izinin sauka a tasoshin jiragen ruwa na Isra’ila ba, kuma za a hana jiragen sama na Isra’ila damar shiga sararin samaniyar Turkiyya.
Da yake magana a wani zama na musamman na Majalisar Dokokin Turkiyya a ranar Jumma’a, Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya zargi Isra’ila da aikata laifuka a Gaza da ya bayyana a matsayin “daya daga cikin mafi muni a tarihi na bil’adama.”
“Isra’ila tana aikata laifin kisan kare dangi a Gaza tsawon shekaru biyu, tana watsi da muhimman dabi’un bil’adama a kan idon duniya,” in ji Fidan.